Kwamishinan kuɗi na jihar Borno, Ahmed Ali Ahmed, ya rasu

Allah ya yi rasuwa wa kwamishinan kudi na jihar Borno, Ahmed Ali.

Har yanzu babu cikakken bayani game da rasuwarsa, sai dai majiya mai tushe ta shaida wa manema cewa kwamishinan ya rasu ne a cikin dakinsa a safiyar ranar Litinin.

 
An ce marigayin ya wuce lokacin da ya saba fitowa da safe. Daga nan aka bude kofarsa da karfi inda aka tsinci gawarsa.

 “Oga ba ya nan, ya mutu “Oga ba ya nan, ya rasu da sanyin safiyar yau,” a cewar majiyar.

 Yanzu Gwamna Babagana Zulum ya rasa mambobin majalisarsa guda biyu ke nan cikin shekara guda

More from this stream

Recomended