Ribadu wanda shi ne babban jami’in tuntunba na kamfen din ta-zarcen shugaba Muhammadu Buhari, ya ce aikin yaki da cin hanci da gwamnatin APC ta yi, ya fi duk abin da PDP ta gudanar a tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulki.
“Ka ga mutum shi kadai, duk duniya yana da gida a ko ina, kana da shi a Ingila kana da shi a America, kana da shi a Dubai. Mutumin da ya yi shekara uku ya zo ya kawo canji a rayuwarmu, za ka ce in cire shi, in dawo da wanda ya yi min lalaci, duk irin nadamar da ya yi, ai ni ba wawa ba ne.” inji Ribadu.
Kalaman nasa na zuwa ne kwanakin kadan kafin ‘yan Najeriya su yi zaben shugaban kasa.
Sai dai babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ta ce, kushe ta da APC ke yi, alamu ne na rashin adalci da kuma rashin hujjar rashin cika alkawuran kamfen da hakan ya jefa ‘yan Najeriya cikin kunci.
“A kasar nan, babu tsaro, babu abinci, babu ayyuka, tattalin arzikin kasa ya lalace, matasa sai shaye-shaye, kai har harkokinmu da kasashen waje ya tabu. To idan aka ce wannan gwamnati ta komo ta sake shekara hudu, sai mu ce Najeriya Allah ya sawwake in akwai ta.” Inji Sakataren PDP na kasa, Sanata Umar Tsauri.
Tuni dai hukumar zabe ta fara tura kayayyakin zabe da hakan ke nuna ba damuwar dage zaben kamar yadda aka gani a 2015.