Kungiyar Izalar Kano Ta Bai Wa CP Wakili Kyautar Kur’ani Da Littafan Musulunci

A yau Asabar ne, 16-3-2019, Kwamishinan ÿan sanda na Jihar Kano Muhammad Wakili ya ziyarci shugaban Kungiyar Izala na jihar Kano, Dr. Abdullahi Saleh Pakistan.

CP wakili, ya kai wannan ziyara ne domin girmamawa da kuma samun kwarin gwiwa a ayyukan da yake gabatarwa a wannan jiha tamu mai albarka.

A yayin ziyayar, Dr. Abdullahi Saleh Pakistan ne ya fara gabatar da jawabai na nasiha da jan hankali ga CP Wakili akan ya rike aikinsa hannu biyu-biyu, kuma yasan cewa Allah zai tambayeshi akan dukkan abinda ya gabatar.

“Ka sani cewar dukkan aikin da mutum yake yi, zai iya wakiltar musulunci a wajen, ka yi iyaka kokarinka wajen kare musulinci da aikin da kakeyi. Kuma kayi Adalci a aikinka, domin Allah zai tsayar dakai yayi maka hisabi a kiyama…”
– Inji Dr. Pakistan

Dr. Abdulmudallib Muhammad, shi ma ya dora da nasiha ga CP wakilin, duk dai don fita hakkin shari’a akansa.

Shi ma a nasa bangaren, CP Wakili ya ce ya ji dadin nasihun da Malaman suka gabatar masa, inda ya ce, dama yana bukatar nasiha domin ya samu kwarin gwiwa a inda yake yin daidai, ya kuma gyara inda yake da kusakurai.

”Ni ba na siyasa, ba ni da Jam’iyya, kuma ba zan siyar da lahira ta akan duniya ta ba, balle na siyar da lahirata akan duniyar wani, kun ga babbar asara kenan” – Inji CP Waliki.

CP Wakili ya bukaci malaman Kungiyar Izala, su taya shi addu’a domin dacewa a aikinsa, sannan ya bukaci a ko yaushe idan ya yi kuskure to a gyara masa.

“In nayi abinda ba daidai ba, ku kirani a waya ku gyara min, ko ku aika min da sako, ko kuzo, ko ku aiko ni nazo” Inji Wakili.

A karshe, Dr. Pakistan ya gabatar da kyautar Alqur’ani mai girma, da littattafai na addinin musulunci da Kwamishinan ÿan sandan na Kano.

A madadin Jagororin kungiyar Izala a matakin jiha, muna fatan alkhairi ga kwamishina, kuma muna rokon Allah ya bashi ikon yin adalci tsakanin al’umma.

Daga Awaisu Al’arabee Fagge,
Director, JSM Kano State.
16-3-2019

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...