Kun san me ya sa Atiku ya fadi zabe

Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A halin yanzu dai za a iya cewa an yi ta, ta kare, domin tuni jama’ar Najeriya suka fara mantawa da zaben shugaban kasa da aka gudanar wanda shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi zarra.

Fafatawar da aka yi a zaben ta kunshi ‘yan takara 73 amma jam’iyyu biyu ne suka fi shahara watau jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta kasar watau PDP.

Masana kan harkokin siyasa sun dade suna fashin baki a kan yadda zaben zai kaya ganin cewa dukkanin ‘yan takarar biyu da suka fi shahara watau Muhammadu Buhari da kuma Atiku Abubakar suna da magoya baya a sassa daban daban na kasar.

Amma a karshe Atiku Abubakar ya sha kaye sakamakon wasu dalilai da ke da alaka da dan takarar.

Wadannan dalilai kuwa sun hada da:

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ikirarin sayar da NNPC

Da dama daga cikin al’ummar Najeriya na mamaki kan yadda Atiku Abubakar ya furta kalaman cewa ko da za a kashe shi sai ya sayar da babban kamfanin mai na Najeriya watau NNPC.

Ana ganin kamar subutar baki ce Atiku ya yi da fadin wadannan kalamai amma dan takarar yana sane ya fadi hakan.

Matsalar ita ce bai fito fili ya yi wa ‘yan kasar bayanin me yasa zai sayar da kamfanin ba.

Haka ma bai gamsar da mutane da za su fito su bayyana kwararan hujjoji musamman a gidajen rediyo da talabijin domin wayar da kan jama’ar kasar ba, kuma hakan ya jawo aka yi wa wannan kudurin nasa mummunar fahimta.

Wadannan kalaman da ya yi ‘yan jam’iyyar APC sun yi amfani da su domin kushe Atiku Abubakar wajen yakin neman zabe kuma ‘yan kasar sun amince da hakan.

Abin da dan Najeriya yake kallo shi ne idan an sayar da kamfanin mai na kasar kudin mai zai karu kuma a ganinsa ita kadai ce kadarar da ta rage da yake amfana da ita.

Tun kafin wannan zaben ‘yan kasar na zargin Atiku Abubakar wajen cefanar da manyan kadarorin kasar kamar su kamfanin wutar lantarki na NEPA da kuma kamfanin sadarwa na NITEL.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Guguwar Buhari

Guguwar Buhari kalma ce da ta samo asali tun 2011 a Najeriya a lokacin da shugaban ya fara takara a jam’iyyar CPC.

A Najeriya an yi itifakin cewa babu wani dan takara a tarihin kasar da yake tara jama’a da kuma yake da goyon bayan jama’a kamar Shugaba Buhari.

A 2011 duk da cewa Shugaba Buhari bai samu mulki ba, jam’iyyarsa ta CPC ta ciwo kujeru da dama a fadin kasar, sai kuma a 2015 guguwar ta shugaban kasar ta lashe kujeru kamar wutar daji.

‘Yan kasar na ganin kwatanta Buhari da wani dan takara a wannan lokaci abu ne mai wahala sakamakon irin farin jinin da Allah ya bashi.

Wuraren da ake ganin guguwar Buhari ta kayar da Atiku a jihohi uku ne, da suka hada da jihar Katsina inda Buhari ya samu kuri’u 1,232,133 sai kuma Atiku ya samu 308,056 kusan tazarar kuri’u 924,077 kenan.

Sai a jihar Kano Buhari ya samu kuri’u 1,464,768 sai kuma Atiku ya samu kuri’u 391,593 kusan tazarar kuri’u 1,073,175 kenan aka samu.

Sai kuma a jihar Borno Buhari ya samu kuri’u 836,496 sai kuma Atiku ya samu kuri’u 71,788 kusan bambancin kuri’u 764,708 kenan.

Wannan alama ce ta har yanzu akwai sauran guguwar Buhari a Najeriya kuma bisa dukkan alamu ta rutsa da dan takarar PDP Atiku Abubakar.

  • Zaben shugaban kasa na 2019

Zargin cin hanci da rashawa

Duk da cewa har yanzu a Najeriya babu wata kotu da ta taba gurfanar da dan takarar ta DP Atiku Abubakar gaban kotu, ‘yan kasar da dama suna yi masa zargin cin hanci da rashawa.

Atiku Abubakar dai ya taba zama mataimakin shugaban Najeriya na shekaru 8 karkashin mulkin PDP inda ake zargin a wannan lokacin ne ya azurta kansa.

‘Yan kasar da dama suna zargin cewa ya mallaki kamfanoni da masana’antu da gidaje a fadin Najeriya da kuma kasashen ketare a lokacin da yake da mukamin mataimakin shugaban kasa.

Wannan ne yasa aka samu rashin yarda tsakaninsa da wasu daga cikin ‘yan kasar inda suke ganin cewa ko da ya lashe zaben, zai azurta kansa ne kawai.

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya fito karara a baya inda ya zargi Atiku Abubakar da cin hanci da rashawa, inda yake cewa ba zai iya zuwa Amurka ba domin ya tafka laifi a kasar dake da alaka da karbar rashawa.

Wannan kalamai na Obasanjo duk da cewa ya yi su ne shekaru da dama amma a lokacin wannan zabe sun yi tasiri kwarai dagaske domin kuwa jam’iyyar APC ta yi amfani da wannan domin kara kushe Atiku da kuma bayyanawa Najeriya cewa akwai kashi a gindinsa ta batun cin hanci da rashawa.

Duk da cewa daga baya Atiku ya samu shiga Amurka tare da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, ‘yan kasar da ‘ya’yan jam’iyyar ta APC sun ce Atiku ya shiga Amurkar ne a matsayin mai taimakawa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki shi yasa kasar basu kama shi ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ikirarin azurta abokansa da ‘yan uwansa

Wani abu da Atku ya dauka kamar da wasa ya zama babbar matsala a gare shi shi ne batun da ya yi na cewa zai azurta abokansa da ‘yan uwansa.

Domin ya ce idan ya ci zabe zai azurta su, kuma kalaman sun zamo abin da aka yi amfani da su domin kayar da shi a lokacin zabe.

Akasarin ‘yan kasar sun tsorata da wadannan kalamai na Atiku domin suna ganin cewa kamar Allah ne ya matse bakinsa ya fadi abin da zai yi idan ya samu nasarar lashe zabe.

‘Yan Najeriya na zargin masu mulki da dama a kasar ba ma Atiku kadai ba inda suke danganta su da ‘ramin kura,’ daga ita sai ‘ya’yanta.

Wadamnan kalamai na batun azurta abokansa da ‘yan uwansa sun jawo muhawarara kwarai da gaske musamman a kafafen sada zumunta.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...