Kotun ɗaukaka ƙara ta mayar wa gwamnan Nasarawa kujerarsa

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja a ranar Alhamis ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, saɓanin hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zabe ta zarta.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana Sule na jam’iyyar All Progressives Congress a matsayin wanda ya lashe zaben, yayin da David Ombugad na jam’iyyar Peoples Democratic Party ya zo na biyu.

Sai dai kotun da mai shari’a Ezekiel Ajayi ya jagoranta a wata shari’ar raba gardama ta yanke cewa bisa ga hujjojin da aka samu daga rumfunan zabe daban-daban da ke gaban kotun, Ombugadu ya samu rinjayen kuri’u a zaben.

Amma Sule ya daukaka kara kan hukuncin inda ya bukaci kotun daukaka kara da ta ajiye shi a gefe.

More from this stream

Recomended