Kotun dake sauraron ƙararrakin fyaɗe da kuma cin zarafin matan aure a jihar Lagos ta yankewa wani mai suna, Nuruddeen Nasiru ɗaurin rai da rai bayan da aka same shi da laifin yi wa yarinya ƴar shekara 13 fyaɗe.
Nasiru ya yiwa ƴar maƙocin nasa fyaɗe ne bayan da ya riƙa nuna mata fina-finan batsa wato Blue Film a shekarar 2021.
A lokacin zaman kotun mai gabatar da ƙara ya gabatarwa da kotun shedu uku da suka haɗa da yarinyar da aka yiwa fyaɗen, mahaifinta da kuma ma’aikacin sashen kula da al’umma.
Har ila yau an gabatarwa da kotun jawabin da Nasiru ya yi na amsa laifin da ya yi a matsayin sheda.
Wanda ake ƙara shi ne sheda ɗaya tilo da lauyoyin da suke kare shi suka gabatarwa kotun.
Da take yanke hukunci ranar Alhamis, Abiola Soladoye alkaliyar kotun ta ce masu gabatar da ƙara sun gabatar da ƙwarara kuma gamsassun hujjojin dake nuna cewa an samu wanda ake ƙara da laifin cin zarafi da kuma aikatawa fyaɗe.
Soladoye ta ce wanda ake ƙara ya riƙa nunawa yarinyar fina-finan batsa inda ya aikata lalata da ita ta dubura.