Wata babbar kotun jihar Kano ta yanke wa wani dan kasar China, Frank Geng-Quangrong, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe budurwarsa, Ummukalthuum Buhari.
Ku tuna cewa Quangrong ya kashe tsohuwar budurwarsa ne sakamakon rashin fahimtar juna da suka samu.
An bayyana cewa ana zargin Quangrong da laifin kisan gillar da aka yi mata, amma ya musanta cewa ya kashe ta da gangan.
Ya kuma roƙi mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji na babbar kotun jihar Kano da ya yi masa adalci.