Kotu ta wanke Sule Lamido da ƴaƴansa biyu daga zargin cin hanci

Kotun daukaka kara dake Abuja ta kori kara tare da wanke tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da wasu mutane kan zargin almundahanar kudade.

Alkalan kotun uku karkashin jagorancin mai shari’a, Adamu Waziri a ranar Talata sun bayyana cewa kotun bata da hurumin sauraron karar.

Tun da farko wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta ki yadda da bukatar Lamido da ya nemi kada a tuhume shi a shariar saboda rashin isassun hujjoji.

Lamido ya daukaka kara ya zuwa kotun daukaka kara inda yake kalubalantar hukuncin kotun.

A shekarar 2016 ne aka gurfanar da Lamido da sauran wadanda ake tuhumar su inda ake musu tuhume-tuhume 46 ciki har da almundahanar kudade da yawansu ya kai biliyan 1.351.

Ana tuhumarsa tare da yayansa biyu Aminu da Mustapha da wani mai taimaka masa, Wada Abubakar da kuma wasu kamfanonin hudu da suka hada da Bamaina Holdings Ltd, Bamaina Company Nigeria Ltd, Bamaina Aluminium Ltd, Speeds International Ltd da kuma Batholomew Darlington Agoha.

A

More from this stream

Recomended