Kotu ta wanke Bafarawa daga zargin aikata cin hanci da rashawa

[ad_1]








Wata babbar kotu dake jihar Sokoto ta wanke tsohon gwamnan jihar, Attahiru Bafarawa daga zargin aikata laifin cin hanci da rashawa.

Hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFFC ce ta gurfanar da shi a gabanta inda take zarginsa da aikata almuundahanar kudade.

Sauran waÉ—anda kotun ta wanke sun haÉ—a da kamfanonin Beedash Nigeria Limited, Nasdabap Nigeria Limited, da wasu mutane biyu Nasiru Dalhatu Bafarawa da kuma Salihu Maibuhu Gummi.

EFCC ta zargi Bafarawa da yin almubazzaranci da kuma almuundahanar kudaden gwamnati, a tsakanin shekarar 1999-2007 lokacin da yake kan kujerar mulkin gwamnan jihar.

Bello Abbas, alkalin dake sauraran shari’ar ya yi watsi da dukkanin tuhume-tuhumen da EFCC kewa Bafarawa da kuma mutane, alkalin ya ce hukumar ta gaza gabatar da kwararan hujjoji da za su tabbatar da laifin.

Hukumar ta yi watsi da hukuncin kotun inda tace zata daukaka kara.




[ad_2]

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...