Kotu ta tsare matashi kan zargin lalata da yarinya ƴar shekara 13

Kotun majistare ta Badagry da ke Legas a ranar Alhamis, ta bayar da umarnin tsare wani matashi dan shekara 28, Stanley Amos, da ake zargi da lalata wata yarinya ‘yar shekara 13.

Alkalin kotun, Patrick Adekomaiya, ya bayar da umarnin a tsare Amos a gidan gyaran hali na Awarjigoh da ke Badagry bayan ya ki amsa laifinsa.

Alkalin kotun ya kuma bayar da umarnin cewa a kwafi fayil din karar sannan a aika zuwa ofishin daraktan kararrakin jama’a domin samun shawarwarin shari’a.

Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Ayodele Adeosun, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Satumba, 2024.

Adeosun ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na rana a unguwar Caroline da ke Aradagun, Badagry, jihar Legas.

A cewar mai gabatar da karar, laifin ya ci karo da sashe na 137 da 261 na dokar laifuka ta jihar Legas a shekarar 2015.

Sakamakon haka, Alkalin Kotun, Adekomaiya, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 25 ga watan Nuwamba, 2024, domin yanke hukunci kan neman belin Amos da kuma shawarar lauyan DPP.

More News

Gwamnatin Enugu ta bayyana dalilin sanya haraji kan gawar mutane

Gwamnatin Jihar Enugu a ranar Lahadi tayi ƙarin haske kan matakin da ta ɗauka kan sanya haraji akan gawar mutane dake ajiye a ɗakin...

Ɗan tsohon gwamnan Kaduna Ahmad Makarfi ya rasu a hatsarin mota

Faisal Makarfi dan gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmad Muhammad Makarfi ya rasu. Faisal ya rasu a wani hatsarin mota da ya faru akan hanyar...

Ƴan sanda sun kama mutane 6 da ake zargi da kisan kai da fashi da makami a Gombe

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce a cikin mako guda  jami'an ta sun kama wasu mutane 6 da ake zargi da aikata fashi...

Ƴan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Gyaran Hali na Maiduguri

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce jami'an ta sun kama Kyari Kur ɗaya daga cikin ɗaurarrun da suka tsere daga gidan gyaran hali ...