Kotu ta halasta shan tabar wiwi a Afirka ta Kudu

0

afirka ta kudu


Masu fafutukar halasta shan wiwi sun yi ta sowa bayan hukuncin kotun

Babbar kotun Afirka ta Kudu ta halasta wa mutanen da suka balaga amfani da tabar wiwi a wuraren taruwar jama’a.

Masu fafutukar ganin an rika amfani da tabar wiwi a kasar sun yi ta sowa suna masu cewa “mun samu kanmu yanzu” bayan kotu ta yanke hukuncin wanda ba a taba yin irin sa ba.

Dukkan alkalan kotun sun kuma amince mutane su rika noman tabar wiwi domin su rika sha.

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi adawa da halasta shan wiwi, tana mai cewa shan wiwi yana da “illa” ga lafiyar jama’a.

Har yanzu ba ta yi tsokaci kan wannan hukuncin ba, inda ba za a ja da shi ba.

A watan Afrilu, Zimbabwe ta zama kasa biyu a Afirka, baya ga Lesotho, da ta halasta yin amfani da wiwi a matsayin magani.

Wasu ‘yan kasar Afirka ta kudu uku ne wadanda ake tuhuma bisa amfani da wiwi suka kai kara kotu, suna masu cewa haramta shan wiwin ya tauye hakkinsu na walwala.

Hakkin mallaka:BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here