Kotu ta ba wa EFCC damar kamo Ayodele Oke

0
Hukumar EFCC

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Hukumar EFCC da ke yaki da rashawa a Najeriya ta ce ta samu sammacin kotu domin kama tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta kasar, Ambasada Ayodele Oke da kuma mai dakinsa Folasade.

Wata Sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar EFCC Tony Orilade ya raba wa manema labarai ranar Alhamis, ta ce hukumar ta samu sammacin ne daga wata kotun Tarayya da ke Lagos.

Kotun ce kuma ta bukaci a kamo Mista Oke da maidakinsa, duk inda aka gansu a fadin duniya.

Ana nemansu ruwa a jallo ne dangane da kudi dala miliyan 43 da hukumar EFCC ta samu a wani gida da ke Legas a watan Afrilun 2017.

Mai shari’a Chukwujeku Aneke ne ya bayar da sammanin kamo su bayan ya amince da bukatar da lauyan EFCC ya gabatar. Kuma alkalin ya ce amincewa da bukatar, mataki ne da ya dace.

Sanarwar ta kuma ce ana tuhumarsu ne da aikata laifuka hudu da suka shafi zamba na kudi naira biliyan 13. daya daga cikin laifukan, ya shafi kudaden da aka samu a wani gida da ke unguwar Osborne a Lagos kudu maso yammacin Najeriya.

A watan Yunin da ya gabata ne wata kotun tarayya a Legas ta bai wa gwamnati damar karba da kuma amfani da kudin tun da babu wanda ya bayyana a gaban kotun cewa kudin nasa ne.

A cikin sanarwar da EFCC ta fitar ta ce, kotun ta dage sauraren karar har zuwa 8 ga watan Maris din wannan shekarar, domin sauraren rahoton kama su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here