Kofi daya na giya na iya haddasa shanyewar rabin jiki

spirits, wine and beer on a bar
Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shan barasa kadan ko daidai gwargwado na kara barazanar kamuwa da hawan jini ko kuma yiwuwar samun cutar shanyewar rabin jiki kamar yadda wani binicike ya bayyana.

Wannan binciken dai ya kalubalanci wani bincike da aka gudanar a baya da ya bayyana cewa shan giya sau daya ko sau biyu a rana ba wata matsala bace.

Binciken mujallar ‘The Lancet’ mai fitar da labarai kan sha’anin lafiya ta gudanar da wannan binciken.

Masu bincike a Ingila da China sun yi nazari kan ‘yan kasar China kusan 500,000 a shekara 10.

Masana sun bayyana cewa yakamata mutane su rage yawan barasar da suke sha.

Tuni aka san cewar shan barasa fiye da kima babbar barazana ce ga lafiyar bil adama da kuma yiwuwar samun cutar shanyewar rabin jiki amma duk da haka wasu binciken sun nuna cewa shan barasar kadan na kara lafiya, wasu kuma suka ce babu wani mizanin shan barasa da za a ce mutum ya tsira.

Me binciken ya gano?

Masu binciken wadanda suka hada da jami’o’in Oxford da Peking da kuma Chinese Academy sun gano cewa:

  • Shan barasa sau daya ko sau biyu a rana na kara yiwuwar kamuwa da shanyewar rabin jiki da kusan kashi 10 zuwa 15 cikin 100.
  • Shan barasa sau hudu a rana na kara yiwuwar kamuwa da shanyewar rabin jiki da kusan kashi 35 cikin 100.

Sakamakon wannan binciken, an bayyana shan barasa sau daya a matsayin.
Binciken ya nuna cewa a duk cikin maza 16 cikin 100 da kuma mata 20 cikin 10 ‘yan Ingila za su samu shanyewar jiki a rayuwarsu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Me yasa harda China?

Kasashen da ke gabashin Asia, kasashe ne da ke da amfani kwarai wajen gano tasirin barasa ga bil adama.

Da dama ‘yan kasar China na da kwayoyin halitta a jikkunansu da ke sawa basu cika san mu’amula da barasa ba, a duk lokacin da suka sha sai su ji ba su da lafiya.

Sakamakon hakane yasa akwai bambanci sosai kan yadda ake shan barasa a kasar – maza kadan suke sha kuma matan ma kadan suke sha.

Me hakan ke nufi a gare ni?

Masu bincike sun bayyana cewa babban sakonsu shi ne babu wata kwakkwarar hujja da ke nuna cewa shan barasa kadan ko daidai gwargwado baya kawo shanyewar rabin jiki.

Wannan na nuna cewa shan barasa ko da kuwa ‘yar kadan ce a rana babbar barazana ce ga lafiyar bil adama.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...