Ko Napoli za ta lallasa Arsenal a Emirates?

aRSENAL

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal za ta karbi bakuncin Napoli a wasan farko na daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Europa a ranar Alhamis.

Wannan ne karo na biyu da kungiyoyin za su kara a gasar, inda a kakar 2013-14 a karawar cikin rukuni Arsenal ta yi nasara da ci 2-0 a Emirates, ita ma Napoli ta rama cin da aka yi mata a Italiya.

A irin wannan lokacin a 2017/18, Arsenal ta fitar da CSKA Moscow a Europa League da ci 6-3 a wasan gida da waje da suka yi, yayin da Atletico Madrid ta yi waje da Gunners a karawar daf da karshe.

Napoli ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai ta Uefa Cup da Europa League karo na uku kenan a tarihi.

A wasan daf da karshe aka fitar da ita a 2014-15, inda ta lashe kofin kakar 1988-89 karkashin jagorancin Diago Maradona.

Sai dai Napoli ba ta taba doke kungiyar Ingila a karawar da ta ziyar ce ta ba a gasar ta Zakarun Turai, bayan wasa takwas a Ingila ta yi canjaras daya aka doke ta a fafatawa bakwai.

Napoli ta yi rashin nasara a Ingila a hannun Burnley da Leeds United da Liverpool da Chelsea da Manchester City da kuma Arsenal.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...