Ko kun san ‘yan sandan da sojojin Najeriya suka kashe a Taraba?

Ana ci gaba da musayar yawu kan kisan da sojoji suka yi wa 'yansandan Najeriya uku

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

—BBC Hausa

Duk da dai an saba da ganin an samu sabanin ra’ayi ko kuma rashin fahimta tsakanin ‘yansanda da soji a Najeriyar, amma da alama wannan na takaddama game da hallaka jami’an ‘yan sanda uku a jihar Taraba ya fi jan hankalin al’umma a baya-bayan nan.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya dai na zargin cewa an hallaka jami’an nata uku ne bayan da wasu sojojin suka bude wa wata tawagar ‘yan sandan wuta.

Lamarin ya faru ne a kan hanyar Ibi zuwa Jalingo, kamar yadda ‘yan sandan suka bayyana cewa tawagar ta masu kai daukin gaggawa ce ta Intelligence Response Team (IRT).

Rundunar ‘yansandan ta Najeriya dai ta ce jami’an nata da sojoji suka hallaka na daga cikin mafiya kwazo da hazaka a bangaren bincike na kasar.

Ta ce wadannan jami’an sun kasance cikin tawagar da ta gudanar da bincike-bincike na tsaro masu hadari da kuma muhimmanci ga kasar.

Jami’an su ne:

  • Insp. Mark Edaile, daga jihar Edo
  • Sgt. Usman Danazumi, daga jihar Taraba
  • Sgt. Dahiru Musa, daga jihar Taraba

Ayyukan bincike da jami’an ‘yan sandan da aka kashe suka yi a baya sun hada da:

1. Damko mashahurin mutumin nan mai satar mutane da ake kira Evans.

2. Kamo mayakan kungiyar Boko Haram 22 wadanda aka zarga da hannu a sace daliban makarantar sakandaren ‘yanmata ta Chibok a jihar Borno.

3. Kwato wasu turawa, ‘yan asalin Amurka da Canada, wadanda aka sace a jihar Kaduna.

4. Kama wanda ake zargin shi ne shugaban kungiyar Boko Haram na arewa-maso-yammacin Najeriya, da mabiyansa da dama.

5. Ceto magajin Garin Daura da aka sace, tare da damke mutane 13 da ake zargi da satan sa a jihar Kano.

Tuni dai sifeta janar na ‘yansandan Najeriya IG Adamu Muhammed ya bukaci al’umma su kwantar da hankulansu yayin da ake bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Sai dai yayin da ake gudanar da wannan bincike, rundunar ‘yan sandan ta Najeriya ta jefa wa rundunar sojin kasar wasu tambayoyi da ta ce tana bukatar amsoshinsu domin fayyace gaskiya.

Daga cikin tambayoyin har da yadda suka saki wani da ake zargin sa da kasancewa kasurgumin mai satar mutane.

Rundunar soji ta Najeriya dai ta musa zargin da rundunar ‘yan sandan kasar ke yi na cewa sojoji sun kashe jami’an ‘yansandan ne da gangan.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin sojin Kanar Sagir Musa ya ce sojoji sun yi ba-ta-kashi ne da masu satar mutane, ba tare da sanin cewa jami’an ‘yansanda ne ba.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...