Kare ya ceto jaririn da aka binne da rai

Karen da ya ceto wani jariri

Hakkin mallakar hoto
KHAOSOD

Wani kare a arewacin kasar Thailand ya kubutar da wani jariri sabuwar haihuwa daga wani rami da aka binneshi da rai.

Ana dai zargin mahaifiyarsa ce wadda ta ke da shekara 15 ce ta binne shi.

Yarinyar ta yi hakan ne saboda gudun kada iyayenta su ga jaririn saboda ba su san ta na da juna biyu ba ma ballantana haihuwa.

Mutumin da ya ke da karen, ya ce karen nasa da ya ke kira Ping Pong, ya gano jaririn ne a lokacin da ya ke tona wani rami a wani fili, inda daga nan ne sai ya ci karo da kafar yaron.

Daga nan ne sai ya yi ta haushi har ubangidansa ya gane lallai akwai wani abu da ya ke so sai ya zo wajensa anan ne kuma ya ga har karen ya yi kokari ya janyo kafar jaririn don a gani.

Anan ne ubangidan karen ya maza ya zaro jaririn daga cikin ramin ya kuma garzaya dashi zuwa wani ofishin ‘yan sanda da ke kusa da su.

Nan da nan ba a bata lokaci ba aka garzaya da shi zuwa asibiti aka duba shi aka masa wanka, sannan kuma likitoci suka tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya.

An dai gudanar da bincike, inda daga baya aka gano mahaifiyar jaririn, wadda yanzu haka aka kai ta gidansu gaban iyayenta tare da jaririn nata.

Yanzu dai jaririn na samun kulawar kakanninsa da kuma mahaifiyarsa, kuma tuni ta yi nadamar abinda ta aikata.

Ubangidan karen ya shaida wa wasu manema labarai cewa, karen nasa ya rasa kafa guda bayan da mota ta kade shi, amma kuma duk da haka yana tare da shi saboda biyayyarsa, da kuma yadda yake taimaka wajen kiwon dabbobinsa.

Hakkin mallakar hoto
KHAOSOD

Ya ce, mutanen kauyensu suna son karen sosai.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...