Kano: Yadda salon Abba gida-gida ya ‘rikita’ siyasar 2019

Abba Gida-gida

Hakkin mallakar hoto
PDP

Kamar yadda masu iya magana ke cewa siyasar Kano sai Kano, kuma a ko da yaushe ta kan zo da wani abu sabo, kamar yadda a bana salon Abba gida-gida da makamantansa suka hadu a yunkurin ‘yan hamayya na kifar da jam’iyyar APC mai mulki.

Masu sharhi da dama sun yi hasashen Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai samu wa’adi na biyu cikin sauki ganin yadda rikici ya dabaibaye jam’iyyar adawa ta PDP da kuma tsagin Kwankwasiyya wadanda su ne manyan masu adawa da gamnan karkashin jagorancin mutumin da ya gada Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Amma sai ga wankin hula ya kai APC da Ganduje dare, inda aka tafi zagaye na biyu, kuma PDP ta kasance a gaba da ratar kuri’a 26,655. Kafin daga bisani APC INEC ta bayyana APC a matsayin wave ta lashe zagaye na biyun da tazarar kuri’a 8,982 jumulla.

Masu sa’ido na gida da waje sun yi Allah-wadai da yadda karashen zaben ya gudana, inda suka ce an yi amfani da ‘yan daba da jami’an tsaro hurin muzgunawa da hana ‘yan adawa kada kuri’a, da kuma aringizon kuri’u, zargin da APC da INEC da ‘yan sanda suka musanta.

Sai dai jam’iyyar PDP ta ce za bi kadun batun a kotu, kuma masu iya magana na cewa shari’a kamar mace ce mai ciki wacce ba a san me za ta haifa ba sai an gani tukunna, a don haka komai zai iya faruwa.

Ko ma dai ya ta kaya a kotun, a zahiri take cewa kawo yanzu Ganduje ya sha da kyar, abin da Hausawa ke cewa ya fi da “kyar aka kamani”. Ga wasu daga cikin abubuwan da suka jawowa gwamnan matsala a zabrn har suka kai ga tasirin Abba K Yusuf da jam’iyyar PDP:

Gandollar

Duk da cewa ya samu kuri’u da dama lokacin da ya lashe zabe a karon farko a 2015, Ganduje ya fara bakin jini a idon wasu ‘yan jihar jim kadan bayan hawansa mulki.

Hakan dai ba zai rasa nasaba da rikicin siyasar da ya barke tsakaninsa da mutumin da ya gada Sanata Kwankwaso tun kafin a je ko’ina, da kuma zargin cewa matarsa da aka fi sani da ‘Goggo” tana tasiri matuka a harkokin mulkin jihar.

Rayuwar siyasarsa ta kara shiga cikin rudani tun bayan da fitaccen dan jaridar nan mamallakin jaridar Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar, ya wallafa jerin wasu faye-fayen bidiyo da ya yi ikirarin cewa sun nuna Gwamna Ganduje yana karbar makudan daloli a matsayin cin hanci daga wasu ‘yan kwangila.

Batun da ya sa a ka ringa kiraye-kiraye a gare shi da ya sauka, yayin da wasu kuma suka nemi a tsige shi.

Duk da cewa Ganduje ya musanta zargin, kuma har ya kai batun kotu kan zargin bata masa suna, hakan bai gamsar da mafiya yawan al’ummar jihar da ma na wajenta ba.


Faye-fayen, wadanda sun kai kusan tara, da suka nuna gwamnan na karbar makudan daloli yana zuba wa a aljihu, sun kara masa bakin jini matuka gaya a idon masu zabe da sauran masu fada a ji a ciki da wajen Kano.

Lamarin ya sa wasu malamai masu fada-a ji sun yi hudubobi a kan batun.

Sakamakon ya haifar da zolaya iri-iri a shafukan intanet.

Duk da cewa Ganduje ya yi kokarin kawar da maganar inda ya samu hukuncin kotun da ya hana ‘yan majalisar jiha bincikarsa, batun ya ci gaba da binsa duk inda ya sa kafa.

Kuma yana cikin manyan abubuwan da ‘yan adawa suka yi amfani da su a kamfe dinsu.

Zaman ‘yan-marina da Buhari

Wata majiya mai karfi a fadar Shugaba Muhammadu Buhari ta tabbatar min da cewa shugaban ya nuna matukar rashin jin dadinsa kan bidiyon, musamman bayan da jami’an tsaro suka “tabbatar masa da sahihancinsu”, kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka rawaito.

Wannan ya sa dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da Ganduje, abin da ya sa aka rinka tantamar ko zai je kamfe jihar, ko kuma bai daga hannun gwamnan ba.

A karshe dai ya je, sai dai taron bai yi wani armashi sosai ba, kuma ko da ya tashi daga hannun gwamnan, sai ya ce “Kanawa ga Gandujenku nan.”

Wannan zaman ‘yan marina da ya rinka yi da shugaban, ta sa wasu jama’ar da dama kin zabarsa, sannan ta bai wa masu adawa da shi a cikin APC damar ci gaba da yakarsa.


Abba gida-gida/Kwankwasiyya kowa agent

Wani babban abin da ya taka rawa wurin kara wa Ganduje bakin jini, shi ne yadda ‘yan Kwankwasiyya suka yi aiki tukuru wurin hada kan mutane da jajircewa domin ganin sun sake kwace gwamnatin da suke ikirarin cewa sun kafa amma ta mayar da su ‘yan kallo.

Duk da cewa da dama sun yi fice wurin hadin kai da nuna biyayya ga jagoransu Dr Rabi’u Musa Kwankwaso, kusan za a iya cewa tsarinsu na wannan karon ya bayar da mamaki.

Salonsu na Abba gida-gida ya taimaka matuka saboda ya yi farin jini a wurin mata da matasa wadanda su ne suka fi tasiri wurin kada kuri’a.

Matasa sun mayar da salon wani abin ado kamar yadda aka rinka yi da salon “Jan goro da wuju-wuju da jan baki” a 2011, lokacin da Kwankwaso ya sake lashe zaben gwamna karo na biyu.

‘Kyawawan mata sun taka rawar gani’

A zagayen farko na zaben an ga yadda mata da matasa sun taka rawa wurin kare kuri’un da suka kada ba tare da an biya su ba, kuma wannan kamar wani sabon salo ne da magoya bayan PDP suka bullo da shi.

A karon farko an samu ‘yan mata da yawa “kyawawa da samari ‘yan boko” suna fita suna aikin agent (masu kare akwatu), wadanda hotunansu suka rika yawo a shafukan sada zumunta.

Sun kuma taka rawa wurin kamfe da yin tallace-tallace a shafukan intanet, ba ya ga wakar Abba gida-gida wacce babu shakka ta ratsa gidajen matan aure da daukar hankalin samari da ‘yan mata.

Kwamred Aminu Abdussalam, dan takarar mataimakin gwamna na PDP, wanda kuma ya jagoranci harkar kula da kungiyoyi na kamfe din, ya shaida min cewa tafiya ce da matasa suka karba da kansu ba tare da an basu kudi ba.

“Alhamdulillahi, mutane sun karbi harkar nan tsakani da Allah, kuma babu abin da za mu ce musu sai godiya, ana nuna mana kauna,” kamar yadda ya shaida min a lokacin da ake yakin neman zaben.

Tasirin Kwankwaso

Wasu masu sharhi da dama na ganin raba-garin da Ganduje ya yi da Kwankwaso na sahun gaba a cikin dalilan da suka sa Ganduje ya samu koma-baya a zagayen farko na zaben, duk da cewa da farko an yi hasashen zai iya kai labari, musamman ganin yadda APC ta lashe zaben shugaban kasa da dukkan kujerun majalisun tarayya.

A cewar Malam Kabiru Sufi, masanin siyasa a Kano, irin ayyukan da Kwankwaso ya yi lokacin yana mulki musamman wadanda saka shafi rayuwar talakawa kamar tallafi a fannin ilimi da samar da ayyukan yi, sun sa har gobe mutane da yawa suna kaunarsa.

“Irin daliban da ya kai karatu kasashen waje da wadanda suka koyo sana’o’i daban-daban sun kafa kungiyoyi da yawa na goyon bayan takarar Abba.

“Wasu a cikinsu ma ma’aikatan gwamnatin jiha ne amma sun fito fili sun nuna ba sa tare da Ganduje,” a cewar masanin.

Kungiyoyi irin na “Lafiya Jari, Kwankwasiyya Luxury Car, Adaidaita Sahu, Mahauta, Dalibai, masu Shayi” da suka amfana a lokacin mulkinsa duk sun yi ruwa sun yi tsaki a kamfe din Abba Kabir, kuma sun boyar da gudummawa sosai.

Duk da cewa sakamakon karshe bai yi musu dadi ba, rawar da Abba ya taka ta sake tabbatar da tasirinsa a siyasar Kano, musamman ganin yadda manyan ‘yan siyasa da ke tare da shi saka sauya sheka zuwa APC – wasunsu ma ana jijiberan zaben, in da aka bar shi daga shi sai matasan ‘yan siyasa.

Wasu masu sharhi na ganin ce-ce-ku-cen da aka samu kan sakamakon zaben na karshe da kuma karar da PDP za ta shigar za su kara hada kan ‘yan jam’iyyar da kuma kara musu karin gwiwa domin fuskantar zabuka na gaba.


Manufofi marasa farin jini

Haka nan kuma wasu sun alakanta reguwar farin jinin Ganduje da wasu manufofi da ya aiwatar kamar sake gina wani bangare na kasuwar Kantin Kwari, lamarin da ya bar baya da kura, inda wasu ‘yan kasuwa masu karamin karfi da ma manya suka yi zargin an salwantar musu da runfunansu.Hakazalika an zargi gwamnan da aiwatar da wasu manufofi da ba su yi wa ‘yan kasuwa da dama dadi ba, ciki har da batun kara kudin haraji ga masu kananan sana’o’i, duk da cewa daga baya ya soke wasu daga ciki bayan da zabe ya karato.Wani zargi da aka dade ana yi wa gwamnatin shi ne na gine-gine da rabon filaye barkatar, lamarin da ta sha musantawa.Amma a cewar Malam Kabiru Sufi, duk wadannan sun yi tasiri a zukatan masu kada musamman a cikin birni, inda nan ne lamarin ya fi shafa, kuma anan ne jam’iyyar PDP ta fi samun kuri’u masu yawa.


Dan sandan da ba ya sabo – Mohammed Wakili – ‘Singam’

‘Yan sanda da dama a Najeriya sun yi taurin suna wurin hada baki da masu mulki a lokutan zabe inda ake zarginsu da muzgunawa ‘yan adawa, lamarin da suka sha musantawa.

Sai dai Kwamishinan ‘Yan sanda na Kano Mohammed Wakili da ake yi wa lakabi da ‘Singam”, wanda aka tura shi jihar jim kadan kafin zaben, kawo yanzu ya ciri tuta.

Kusan baki yazo daya tsakanin al’umma wurin yabawa rawar da yake takawa ta yakar ‘yan bangar siyasa, da daba, da kuma nuna ba-sani-ba-sabo a huldarsa da ‘dukkan bangarorin siyasar kasar.

Rahotanni sun ce an yi kokarin sayensa da kudi domin ya bari a yi magudi amma ya yi ki amincewa.

Sai dai a wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta na wani jawabi da ya yi a wani wurin tattara sakamaon zabe, ya ce ai shi ba wanda zam kuskura ya tunkare shi da cin hanci.

Tsayuwar-dakan da ya yi ta fito fili ne bayan da jami’ansa suka cafke manyan jami’an gwamnati bayan da aka zarge su da kawo cikas wurin bayyana sakamakon zaben Nasarwa – inda PDP ta lashe.

Wannan ya sa sunansa ya zama daya daga cikin maudu’an da aka rinka tattaunawa a kansu a shafukan sada zumunta, inda mutane suka rinka yaba masa.

Wani tsohon babban jami’in ‘yan sanda da ya nemi na sakaya sunansa ya shaida min cewa a ‘yan shekarun baya-bayan nan ba zam Iya tuna wani dan sanda da ya samu karbuwar jama’a ba kamar CP Wakili.

Sannan ya kara da cewa shi ne “silar samun nasarar jam’iyyar PDP a zagayen farko na zaben, domin da bai jajirce ba, to sai an murde sakamakon zane”.

Sai dai ba a ji duriyarsa ba a lokacin da aka zo kammala zaben a ranar 23 ga watan Maris, duk da irin tashin hankalin da aka samu a mafi yawan wuraren da zaben ya gudana.

Wasu kafafen yada labarai sun rawaito cewa hakan ba zai rasa nasaba da “kwace ikon da aka yi daga hannunsa ba inda a mika komai ga mataimakin sufeto janar da wasu manyan jami’ai da aka tura jihar daga Abuja”.

Fatan da jama’a da dama ke yi shi ne CP Wakili ya zamo zakaran gwajin-dafi ga sauran ‘yan sandan kasar, kuma ya dore a kan wannan manufar tasa ta “tsayawa kan gaskiya”.

Game da siyasar Kano da kuma musayar yawu kan zaben na bana, za a iya cewa yanzu aka fara, domin kowanne irin hukunci kotu ta yanke kan lamarin, ba zai kawo karshen ce-ce-ku-ce ba.


More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...