Kamfanoni Guda 4 Sun Fara Samar Da Madara A Najeriya

Duk a cikin manufar babban bankin Najeriya wato CBN na hana shigo da madara daga waje, wasu kamfanonin kasar guda hudu sun soma sarrafa madara yar gida.

Gwamnan CBN Godwin Emefiele wanda ya bayyana hakan a Abuja a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba, ya bayar da sunayen kamfanonin.

KamfaNonin sune FrieslandCampina WAMCO, Neon Agro, Chi Limited da Irish Dairy. Yace sun rigada sun nuna ra’ayin zuba jari a kamfanin Bobi Grazing Reserve a jihar Neja.

Bobi Grazing Reserve dake a yankin karamar hukumar Mariga ya kasance daga cikin masana’antun kiwo 26 karkashin wani shirin bunkasa harkar kiwo da gwamnatin jihar Neja ke yi tare da hadin gwiwar CBN.

A halin yanzu gwamnan CBN yace FrieslandCampina WAMCO da Neon Agro sun amince da kowannen su zai siya fili mai fadin hekta 10,000, sannan Chi Limited da Irish Dairy zasu siya hekta 4,000 kowannen su don kafa shirin sarrafa madara.

Gwamnatin jihar zata ajiye sauran hekta 3,000 don gudanar da shirin cigabanta.

A ranar Talata, 18 ga watan Satumba, Mista Emefiele yace kamfanin FrieslandCampina WAMCO ta gyara fili hekta 695 sannan anyi shuke shuke a hekta 190 don shirin kiwo.

Har ila yau, kamfanin ta kammala shuke shuken iri masu inganci, famfunan solar yayin da ake jiran hada kayan aikin tatse madara.

A wani lamari makamancin haka, yace Chi Limited har ila yau ta sa hannu a kwangilan shuke shuken fili hekta 4,000 da aka samar mata.

Yace Gwamnatin Jihar Neja ta gyara da kuma katange hekta 63 a wurare biyu.

Yace wurin zai kasance da cibiyar yan sanda, asibitin dabbobi, makarantar firamare, yayinda ake shiri gina cibiyar lafiya. hakazalika a yazu aa kan shuke-shuke.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...