Kalaman Buhari a kan satar kuri’a ta tayar da kura

Shugaba Muhammadu Buhari

Hakkin mallakar hoto
TWITTER/@BASHIRAHMAAD

‘Yan Najeriya na ci gaba da yin muhawara a game da gargadin da shugaban kasar ya yi cewa duk dan siyasar da ya yi yunkurin satar kuri`a a manya zabukan kasar da ke tafe, to ya yi ne a bakin ransa.

Tuni dai babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta soki wadannan kalaman na shugaban kasar a cikin wata sanarwa da ta fitar.

PDP ta ce tana fatan wannan kiran da shugaban ya yi ba wata makarkashiya ba ce ta bai wa wadanda ta kira sojojin bogi da jam’iyyar ta tattara damar harbe ‘yan Najeriya su kuma kwace akwatunan zabe su yi aringizon kuri’u a ranar zaben.

Abdullahi Umar, wani dan Najeriya ne da ke cewa shi a ra’ayinsa tun da Najeriya kasa ce da dokoki ya kamata a bi doka wajen yanke hukunci a kan kowanne irin laifi.

Abdullahi ya ce yin karan tsaye da tsallake abin da kundin tsarin mulki ya tanadar ka iya jefa rayukan ‘yan kasa cikin hadari kasancewa ba a taru an zama daya ba.

Shi ma ana sa ra’ayin Ahmed Usman, ya ce wannan ra’ayi ne irin na shugaban kasa domin akwai hanyoyi da dama da za a iya bi wajen dakile satar kuri’a ba sai ta hanyar harbi ko barazana ga rai ba.

Sai dai kwamitin kamfe na Shugaba Buhari a ta bakin Honourable Faruk Adamu Aliyu, ya ce an yi wa kalaman shugaban mummunar fahimta.

A ranar 16 ga watan Fabrairun 2019 ne hukumar zaben Najeriya ta dage babban zabenta sa’o’i kalilan kafin fara zaben.

Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce daga wasu daga cikin ‘yan kasar da ma jam’iyyun siyasa bisa dage wannan zabe sa’oi kadan kafin a fara gudanar da shi.

More News

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...

Hukumar NDLEA ta lalata sama da tan 300 na miyagun kwayoyi da aka kama a Legas da Ogun

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi nasarar lalata kilogiram 304,436 da lita 40,042 na haramtattun abubuwa da...