Kaduna: An hallaka mutum 66 a jajibirin zabe

Malam Nasir el-Rufa'i

Hakkin mallakar hoto
@elrufa’i

Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ba sun kashe akalla mutane 66 a karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna a ranar Juma’a.

Gwamnatin Kaduna da ta tabbatar da labarin ta ce harin ya fi shafar mata da yara kanana, inda aka kashe yara 22 da mata 12.

Harin kuma ya shafi rugagen Fulani da dama da ke cikin karamar hukumar Kajuru da suka hada da Ruga da Bahago da Ruga Daku da Ruga Ori da Ruga Haruna da Rugar Yukka Abubakar da Ruga Duni Kadiri da Ruga Shewuka da Ruga Shuaibu Yau.

Gwamnatin Kaduna ta yi Allah wadai da harin, inda gwamnan jihar Nasir el-Rufa’i a cikin wata sanarwa da ya wallafa a Twitter ya bayyana cewa ya tura jami’an tsaro a yankin.

Kuma gwamnan ya ce tuni aka kama wasu daga cikin maharan.

An kai harin ne a jajibirin zabe, inda ‘yan Najeriya ke shirin kada kuri’ar zaben shugaban kasa.

Karin bayani na tafe…

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...