Kungiyoyin kwadago da masana’antu da masana tattalin arziki da kudi da shari’a sun gargadi gwamnatin tarayya da kada ta cire tallafin wutar lantarki kamar yadda asusun lamuni na duniya IMF ya shawarta.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur, bisa shawarar IMF da bankin duniya.
Sai dai, asusun, a rahotonsa na baya-bayan nan, ya shawarci gwamnati don ta kawar da tallafin man fetur da wutar lantarki gaba daya a matsayin wani mataki na magance kalubalen tattalin arzikin da ake fuskanta.
A cikin rahotonta mai taken ‘IMF Executive Board Concludes Post Financing Assessment with Nigeria,’ IMF ta nanata muhimmancin kawar da tallafin don karkatar da albarkatun zuwa shirye-shiryen jin dadin jama’a.
A halin da ake ciki na tsadar rayuwa, IMF ta ba da shawarar tura wa jama’a tallafi don ba da taimako na wucin gadi ga ɓangarorin al’ummar Najeriya masu rauni.