Ka san me yake sa ‘yan siyasa yin alkawarin bogi?

Matasa a Najeriya na zargin 'yan siyasa da kin cika alkawurra

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A yayin da lokacin zabe yake karatowa, ‘yan siyasa kan rinka yawo don yakin neman zabe domin ganawa da al’umma da kuma shaida masu irin ayyukan da suke da niyyar aiwatarwa idan sun samu kujerar da suke nema.

Wani matashi a Najeriya, Bello Bala Shagari ya ce da yawa irin wadannan alkawurra da ‘yan siyasar kan yi kan tafi ne ba tare da an aiwatar da su ba.

A cewarsa “Yawanci ‘yan siyasa ba su cika kashi hamsin zuwa sittin na alkawurran da suke yi.”

Ya kara da cewa hakan na faruwa ne saboda ‘yan siyasar na yin alkawurran ne ba tare da yakinin cewa za su iya cika su ba.

“‘Yan siyasa sukan yi alkawurra, har da wadanda ba su san yadda za su cika su ba.”

Sau da yawa sukan yi alkawurran, amma a lokacin da suka ci zabe sai su gane cewa ba za su iya cikawa ba-In ji Shagari

“‘Yan siyasar kan yi irin wadannan bayanai ne saboda suna neman kuri’a ko kuma saboda suna tunanin ayyukan na da sauki.”

Wata matashiya a Najeriya Hafsatu Umaru Shinkafi ta ce ‘yan siyasa kan yi wa mata dadin baki a lokacin yakin neman zabe.

Sai dai ta ce matsalar da ake fuskanta ita ce akan manta da matan da alkawurran da aka masu bayan an ci zabe.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...