Jami’an tsaro sun sake kama wani kusa a jam’iyar PDP a Kaduna

Jami’an tsaro sun kama Yaro Makama, jigo a jam’iyar PDP ta jihar Kaduna.

Kamun nasa na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da aka kama, Ben Bako daraktan yada labaran yakin neman zaben jam’iyar PDP a Kaduna aka kuma tasa keyarsa a jirgin sama ya zuwa birnin tarayya Abuja.

An kama Bako ne saboda yin kalaman tayar da hankali cikin wani fefan bidiyo da aka dauka a lokacin da jam’iyyar ta ke gangamin yakin neman zabe a garin Kafanchan dake karamar hukumar Jama’a a makon da ya gabata.

Da yake magana kan lamarin mataimakin daraktan yakin neman zaben jam’iyar, Danjuma Sarki ya bayyana cewa wannan wani shiri ne na murkushe ƴaƴan jam’iyar gabanin zabe mai zuwa..

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...