Jami’an kwastam sun kama wata kwantena makare da kayan sojoji

[ad_1]
Hukumar hana fasa kwauri ta kasa wato kwastam ta tsare wata kwantena dake makare da kayan sojoji akan hanyar Aba zuwa Fatakwal.

Joseph Atta, mai magana da yawun hukumar ta kwastam ya sanar da cewa jami’an hukumar dake Shiyar C sune suka tare kwantenar ranar Juma’a.

“An dauki kwantenar ya zuwa Owerri inda aka gudanar da cikakken bincike a gaban wakilan mai kayan an samu dila 11 da dake dauke da dinkakkun kayan sojoji, ” Atta ya ce a cikin sanarwar da ya fitar.

Ya kara da cewa kowacce dila na ɗauke da setin kaya guda 400 dinkakku da kuma katon 15 na takalmin sojoji.

Tuni dai aka tsare wakilan mai kayan inda ake cigaba da gudanar da bincike.
[ad_2]

More News

An Jikkata Jami’an Tsaro A Harin Da Ƴan Bindiga Su ka Kai Wa Ayarin Motocin Yahaya Bello

A jikkata wasu jami'an tsaro a wani hari da yan bindiga su ka kai kan jerin ayarin motocin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ranar...

Bala Muhammad ya zama shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP

An zaɓi gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad a matsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP. Siminalayi Fabura zaɓaɓɓen gwamnan jihar Rivers shi ne mataimakin shugaban...

Za mu sake bitar mafi karancin albashi a Najeriya—Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin sake nazarin mafi karancin albashin ma’aikata domin dacewa da yanayin tattalin arzikin kasar nan. A cewarsa, akwai bukatar...

EFCC na zargin tsohuwar ministar mata a mulkin Buhari da karkatar da naira biliyan 2

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta titsiye tsohuwar ministar harkokin mata Pauline Tallen kan zargin azurta kai ta...