Connect with us

Hausa

Itacen girki na karanci a Maiduguri

Mayakan Boko Haram sun sha kai harin kunar bakin wake kan al'umma a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A garin Maiduguri babban birnin jihar Borno, da ke arewa-maso-gabashin Najeriya jama’a na kokawa game da karancin itacen girki da kuma gawayi.

To ko me ya jawo hakan?

Wani mutum da ya dogara da sana’ar shigo da itacen girki da gawayi daga wasu jahohin na Najeriya ya ce jami’an tsaro kan hana motoci masu dauke da itacen ko kuma gawayi shiga birnin na Maiduguri.

A cewarsa ‘Amma na ji an ce an dauki wannan mataki ne saboda tsaro.’

Ya kuma kara da cewa a yanzu itacen girki da ake sayarwa Naira 250 ya kara farashi zuwa Naira 300.

Jihar Borno dai ita ce a tsakiyar matsalar tsaro na rikicin Boko Haram, wanda aka kwashe sama da shekara 10 ana fama da shi.

A kwanakin baya, mayakan Boko Haram sun rinka amfani da daidaikun mutane ko yara mata wajen kai harin kunar-bakin-wake kan al’umma a birnin Maiduguri.

A baya-bayan nan kuma mayakan sun tsananta kai hare-hare kan sojojin Najeriya, gabanin babban zaben kasar na shekarar 2019.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Ƴanbindiga sun kashe shugaban jam’iyar APC a jihar Imo

Yan bindiga sun harbe, Mista Ifeanyi Ozoemena,shugaban jam’iyar APC na mazabar Logara/Umuohiagu dake karamar hukumar Ngor Okpala ta jihar Imo.

Wakilin jaridar Daily ya tattara bayanan dake cewa an harbe Ozoemena har lahira ranar Talata da daddare sa’o’i biyu bayan da ya jagoranci taron jam’iyyarsa a mazabarsa a shirye shiryen da suke na tunkarar zaben shugaban dana yan majalisun tarayya.

A cewar wadanda suka sheda abinda ya faru, an harbe shugaban na APC a cikin gidansa lokacin da iyalansa ke tare da shi.

Mataimakin shugaban kungiyar cigaban al’ummr Logara wanda ya tabbatar da faruwar kisan kan da ya bayyana da abu marar dadin ji.

Kwamishinan ƴansandan jihar, Dasuki Galadanchi ya tabbatar da faruwar lamarin a tattaunawar da ya yi da wakilin jaridar Daily Trust ta wayar tarho inda ya ce tuni jami’an tsaro suka dauke gawar.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Man City ta nuna wa Schalke 04 kwanji

Man City

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Manchester City ta yi nasarar doke Schalke 04 da ci 3-2 a wasan farko zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League da suka kara ranar Laraba.

City ce ta fara cin kwallo ta hannun Sergio Aguero, daga baya Schalke ta ci biyu duk a bugun fenariti ta hannun Nabil Bentaleb.

Bayan da aka dawo daga hutu ne City ta farke ta hannun Leroy Sane a bugun tazara, sannan Rahem Sterling ya ci na hudu.

City ta kare karawar da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka korar mata Nicolas Otamendi a minti na 23 da komawa zagaye na biyu.

Schalke 04 za ta ziyarci Ettihad domin karawa da Manchester City a wasa na biyu a ranar 12 ga watan Maris.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Gobara ta kone shaguna 31 a kasuwar Gumi dake Kaduna

Jumallar shaguna 31 da kuma kayan abinci na miliyoyin naira gobara ta kone kurmus ranar Laraba a kasuwar Sheikh Gumi dake yankin Bakin Dogo a jihar Kaduna.

An gano cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 2:00 na dare lokacin da masu shagunan ke kwance a gidajensu sai dai masu gadi kawai a kasuwar.

Ya zuwa yanzu babu cikakken bayanin musabbabin faruwar gobarar amma yan kasuwar sun alakanta tashin gobarar da wutar lantarki.

Gobarar tafi shafar bangaren masu sayar garin rogo dana masara akan titin Birnin Kudu dake yankin Bakin Dogo.

Da wakilin jaridar Daily Trust ya ziyarci wurin ya iske masu alhini da kuma masu shaguna sunyi rukuni-rukuni suna tattaunawa kan faruwar lamarin.

Shugaban masu sayar da Rogo a Bakin Dogo, Alfa Hussaini ya ce yan kasuwar na bukatar tallafi.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: