INEC ta ba wa ‘yan Najeriya hakuri

Mahmud Yakubu

Hakkin mallakar hoto
Facebook

Image caption

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ba wa ‘yan kasar hakuri bayan da ta dage zaben da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar.

An dage babban zaben shekarar 2019 ne sa’o’i kalilan kafin fara shi, inda aka dage shi zuwa ranar 23 ga watan Fabrairun shekarar 2019.

Wani darakta a hukumar zaben kasar Festus Okaye ya ce har bayan karfe 12;00 na daren ranar Asabar hukumar tana da tabbacin za ta iya gudanar da zaben.

Jami’in ya ce sun samu matsala ne akalla a bakwai daga cikin jihohi 36 da ke fadin kasar.

Mista Festus ya ce hukumar zaben ta yi takaicin abin da ya faru kuma saboda haka tana neman afuwa daga ‘yan kasar.

Daga nan ya ba da tabbacin cewa hukumar zaben ta dukufa wajen ganin ta gudanar da zaben kamar yadda aka tsara a mako mai zuwa.

Ya bukaci ‘yan kasar da su ba hukumar goyon baya don ganin ta gudanar da sahihin zabe.

Mutane da dama ne suka rika bayyana rashin jin dadinsu da matakin da hukumar ta dauka na dage zaben a ranar Asabar, musamman a kafafen sada zumunta.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...