Hukumar Zabe ta kasa INEC, ta ce a yanzu jam’iyun siyasa za su iya cigaba da yakin neman zabe gabanin sabuwar ranar da aka saka ta zaben shugaban kasa.
Hukumar ta bayar da wannan umarnin ne bayan wani taro da tayi ranar Litinin a Abuja.
Tun da farko shugaban hukumar, Mahmoud Yakubu ya ce ba za a cigaba da yakin neman zabe ba duk da dage ranar zaben shugaban kasa da na yan majalisun tarayya da aka yi.
Amma kuma bayan zaman ganawar da shugabannin hukumar suka yi hukumar ta ce yan takarar shugaban kasa da kuma jam’iyun siyasa za su cigaba da yakin neman zabe har ya zuwa daren ranar Alhamis.
Ko da a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC da ta gudanar a yau jam’iyar taci alwashin cigaba da yakin neman zabe duk da cewa hakan yaci karo da umarnin INEC.
Dokar zabe ta bayyana za a dakatar da yakin neman zabe ne sa’o’i 24 gabanin a fara kada kuri’a.