Ina gaskiyar batun dauke CP Wakili daga Kano?

Tun bayan da aka gudanar da zaben gwamnoni a jihohi 29 a Najeriya, jama’a da dama na ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta a kan cewa rundunar ‘yan sandan kasar ta dauke kwamishinan ‘yan sandan Kano Mohammed Wakili ta kai shi wata jihar domin ci gaba da aiki.

Mai magana da yawun ‘yan sandan reshen jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya shaida wa BBC cewa wannan labarin da ake yada wa ba gaskiya ba ne.

Jama’a da dama a shafukan sada zumunta sun ta mayar da martani kan wannan lamarin tun bayan da aka fara yada wannan jita-jitar.

Wadannan wasu ne daga cikin zantuttukan da ake yi a shafin Twitter kan batun dauke Wakili daga Kano.

Jama’a da dama a Najeriya sun jinjinawa Mohammed Wakili kan irin tsayuwar daka da ya yi a lokacin zaben gwamna da ‘yan majalisar jihar Kano da aka gudanar a ranar Asabar.

Shi ma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na ll ya jinjinawa kwamaishinan kan irin zage damtsen da ya yi wajen kare dukiyoyi da rayukan jihar Kano.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Jama’a su kwantar da hankali – Sarkin Kano

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Wani mutumi ya kashe mahaifiyarsa a kan kudi

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mazaunin kauyen Kajola da ke kusa da Apomu a jihar mai suna Lukman Adejoju bisa...

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Rundunar dakarun soja ta ƙasa da ƙasa wato Multi National Task Force(MNJTF) a turance shiya ta 3 dake Monguno a Najeriya ta bayar da...

Sojoji a birnin Ibadan  sun kama Æ´an fafutukar kafa Æ™asar Oduduwa

Dakarun rundunar sojan Najeriya  sun samu nasarar kama wasu mutane masu fafutukar kafa ƙasar Oduduwa a birnin Ibadan na jihar Oyo. Masu fafutukar sanye da...