Hotunan taron yaƙin neman zaben ɗan takarar sanata na mazabar arewacin Katsina a jam’iyar PDP

 

Jam’iyar ta gudanar da taron gangamin yakin neman zabe na dantakarar sanata a zaben cike gurbi da za a gudanar ranar Asabar.

Zaɓen zai gudana ne biyo bayan rasuwar sanata mai wakiltar mazabar, sanata Mustapha Bukar.

Taron gangamin na jam’iyar PDP ya gudana a garin Kankia inda ya samu halartar jiga-jigan jam’iyar PDP da suka fito daga jihohin kasarnan daban-daban.

Cikin jiga-jigan sa suka halarta akwai sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, toshon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema da sauran mutane da dama.

 

 

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...