Har yanzu ba a sako Alaramma Ahmad Sulaiman ba, jita-jita ne kawai – Datti Assalafy

0

Mutane da yawa sun dameni da tambaya wai sunga ana yayata labarin cewa Alaramma Ahmad Suleman Kano da abokan tafiyarsa sun kubuta daga hannun wadanda sukayi garkuwa dasu…

Wannan maganar ba gaskiya bane, Malam yana hannunsu har zuwa yanzu da nake rubutu, kuma wadanda sukayi garkuwa dashi sunyi magana, sun bukaci a basu makudan kudi na fitar hankali, lamarin akwai cin amana da hadin baki, amma ba zan bayyana muku ba saboda dalilai na bincike

Babban abin damuwa da tashin hankali shine Alaramma Ahmad Suleman Kano bashi da lafiya tunda jimawa yana fama da rashin lafiya, a yanzu haka ya na shan magunguna, lokacin da kidnappers din suka kamashi basu bari ya dauki maganin da yake sha ba, sun bar maganin a cikin motarsa, kawai shi suka dauka suka tafi dashi tare da abokan tafiyarshi suka bar motar a gefen titi

Mu wannan rashin lafiyar shine babban abinda yafi tayar mana da hankali game da Malam, domin mutum ne da yake shan magani a dalilin jinyar da yake fama da ita kuma an rabashi da magani

Hakika wadannan mutanen banza azzalumai sun taba kayan Allah, domin Mahaddata Qur’ani kayan Allah ne, ba zasu wanye lafiya ba insha Allah

Muna rokon Allah da sunayenSa Tsarkaka AL-HAYYU AL-QAYYUM Ya kubutar mana da Malam tare da abokan tafiyarsa Amin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here