Hanyar yaki da cutar Maleriya a wannan zamanin

Mosquito feeding

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani babban rahoto da aka fitar na nuni da cewar duniya za ta iya cimma nasarar zama ba tare da cutar Malaria ba, daya daga cikin dadaddiya kuma muguwar cutar da ke shafar al’umma a wannan zamanin.

Har yanzu a kowace shekara, ana samun fiye da mutum miliyan 200 da cutar ke kamawa, wacce ta fi yawan kashe yara.

Rahoton ya ce kawar da cutar baki daya abu ne mai yiyuwa, sai dai, ana bukatar karin kudi da suka kai dala biliyan biyu wato domin zuba kudin da zai kawar da kwayar cutar.

Masana dai sun ce kawar da cutar abu ne mai girma sosai.

Mece ce cutar Malaria?

Cutar Malaria, cuta ce da ke samuwa ta hanyar wasu kwayoyi da ake kira “Plasmodium” .

Wadannan kwayoyin cutar na yaduwa ne daga mutum zuwa mutum idan macen sauro ta ciji mutum a yayin da take neman abincinta wato jini.

Da zarar mutum ya kamu da cutar, tsananin zazzabi ne zai rufe shi.

Kwayoyin na cutar da hanta da kuma kwayoyin halitta na jini wadanda ke samar da tsaftatacciyar iska zuwa jiki ya kuma fitar da gurbatacciya wato “red blood cells” da kuma sa karancin kwayoyin halitta na jini.

Daga bisani cutar na cinye jiki baki daya, har da kwakwalwa har ma ta kai ga kisa.

Ana samun mutuwar mutum 435,000 a kowace shekara wadanda yawanci yara ne.

Kawo yanzu me ake ciki?

An samu gagarumar nasara wajen yaki da cutar malaria a duniya baki daya.

Tun a shekarar 2000:

  • Yawan kasashen da ke fama da cutar malaria ya ragu daga 106 zuwa 86
  • Yawan cutar ya yi kasa da kashi 36 cikin 100
  • Yawan mace-mace ya yi kasa da kashi 60 cikin 100

An samu cimma wadannan nasarorin ne saboda yawan samun hanyoyin hana cizon sauro kamar amfani da gidan sauro wanda aka sanya wa magani da kuma nagartaccen magani ga wadanda suka kamu da cutar.

Duk da wadannan nasarori da aka samu, cutar malaria dai ta cigaba da shafar wasu al’ummomi a sassan duniya a kasashe masu tasowa, in ji Dakta Winnie Mpanju-Shumbusho, daya daga cikin marubutan rahoton.

“Wannan zance tabbatace ne musamman a nahiyar Afirka, inda kasashe biyar kawai ke dauke da alhakin hakan na kusan rabin sauran kasashen duniya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sauro ne ke haddasa maleriya

Meye sa wannan rahoton ke da amfani?

Cimma nasarar kawar da cutar Malaria baki daya a doron kasa zai zama wani abu gagarumi na tarihi.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kaddamar da rahoton ne shekara uku da suka gabata domin sanin yadda yakin zai kasance da kuma nawa za a kashe.

Mutum na 41 a jerin kwararru kan cutar Malaria a duniya kama daga ilimin kimiyya da na tattalin arziki, ya ce za a iya cimma hakan nan da shekarar 2050.

Ana kamanta rahoton su wanda aka wallafa a Lancet a matsayin irin sa na “farko da aka taba yi”.

Daya daga cikin mawallafan rahoton, Sir Richard Feachem, ya ce an dade ana ta mafarkin kawar da cutar Malaria a doron kasa, amma a yanzu, sun ce suna da hujjar cewa za a iya, kuma ya kamata a kawar da cutar nan da shekara 2050.

“Wannan rahoton na nuna cewar kawar da cutar abu na mai yiyuwa a wannan lokacin.”

Sai dai kuma yayi gargadin cewa samuwar sai an yi da gaske kafin hakan ya samu.

Me ake bukata domin cimma hakan?

Rahoton ya yi hasashen cewa duba da abubuwan da suke da shi a kasa, da yiyuwar za a iya kawar da cutar Malaria da babban kaso nan da shekarar 2050.

Sai dai za a iya samun kangarewa a nahiyar Afirka kama daga kasar Senegal a arewa maso yamma zuwa kasar Mozambique a kudu maso yamma.

Don kawar da cutar nan da shekarar 2050, ana bukatar karin amfani da fasahohin da ake da su yanzu yadda ya dace, da kuma samar da wasu sababbin hanyoyin yaki da ita.

Sabanin dabi’un yau da kullum na kwayoyin halitta na gado, fasahar sauya kwayoyin halitta na wajabta wa wata kwayar halitta ne ta yadu a tsakanin dangoginta.

Hakan zai iya sa macen sauron ta kasa daukar ciki wanda zai jawo rugujewar yawan su, ko kuma hana su kamuwa da kwayar cutar.

Sarkin Mswati na uku na kasar Eswatini (kasar Swaziland a da) kuma jagora na shuwagabannin Afirka kan yaki da cutar Malaria ya ce kawar da cutar Malaria da dangoginsa abun sa wa a gaba ne wanda ya kamata a cimma masa.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

King Mswati III na Eswatini

Ana ta fafutukar ne domin cimma yaki da sauron da ke dauke da kwayar cutar malaria, wanda duka biyun suna cigaba da habaka ne wajen yaki da cutar.

Ya ce sai sun tabbatar da cewar, an bai wa kirkire-kirkire muhimmanci.

Nawa za a kashewa duka wannan?

A halin da ake ciki yanzu, rahoton ya kiyasta cewar ana kashe kusan dala biliyan 4.3 wato kudi yuro biliyan 3.5 a kowace shekara.

Amma ana neman karin dala biliyan biyu a kowace shekara domin kawar da cutar a duniya baki daya nan da shekarar 2050.

Marubutan sun ce akwai kuma kasafin hada-hada kamar yadda aka saba wanda ya shafi rasa rayuka da mutane ke yi da kuma nacin fafutukar yaki da kwayar cutar da kuma sauron da ke fito da sababbin hanyoyin kin jin magungunan hadiya da kuma na kashe su.

Rahoton ya ce samun karin dala biliyan biyu a shekara zai zama babban kalubale, sai dai in aka duba, za a ga alfanun yin hakan zai fi kudin.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kwanciya cikin gidan sauro na kare mutum daga cizon sauron

Za a iya kawar da cutar malaria nan da shekarar 2050?

Kawar da cuta a doron kasa baki daya kalubale ne babba.

Ya taba faruwa sau daya kafin mutane su kamu da cutar- an taba ayyana cewa babu cutar karanbau a shekarar 1980.

An hada karfi da karfe da kuma ingantattun magunguna domin cimma hakan.

Sai dai akwai wani dalilin da yasa cutar karanbau ta kasance daya tilo da kuma a tarihin cutar shan inna wanda ke nuni na kalubalen da kawar da cutar ke da ita.

A ganin nasarar da aka samu na kawar da cutar karanbau, sai aka sa ran cewar cutar shan inna ma zai shiga tarihi a shirin dakile cutar da aka yi na shekarar 2000.

Bayan shekaru 21 da sanya shirin dakile cutar da kuma yawan kamuwar cutar da kashi 99 cikin 100, kashi daya daya rage a cimmawa ya yi turjiya matuka.

Najeriya da kuma nahiyar Afirka baki daya na gab da kawar da cutar shan inna, sai dai sun kasa samar da maganin ga yara a kasashe biyu da ke fama da yaki wato Pakistan da kuma Afghanistan.

Me mutane ke cewa akan hakan?

Shugaban WHO Dr Tedros Ghebreyesus, ya ce kawar da cutar Malaria ya kasance daya daga cikin manyan abun da al’umma ke son ganin an cimma shekaru da dama, sai dai kuma ta kasance cutar da ta fi kowace cuta fuskantar kalubale.

Sai dai ba za a cimmakawar da cutar ba a lokacin da ake sa rai da yadda aka nufo shi da kuma kayan aikin da ke kasa wanda da yawan su an yi su ne a shekarun baya da suka wuce ko ma kafin nan.

Dakta Fred Binka na Jami’ar kiwon lafiya da kimiyya dake Ghana ya ce kawar da cutar malaria muhimmin abu ne.

Ya ce yana bukatar ba shi muhimmanci da jajircewa da kuma hada gwiwa kamar ba a taba yi ba, duk da cewar mun san cewar alfanun ya fi kudin yawa ba wajen ceto rayuka kawai ba, har ma da inganta walwalar mutane, karawa tattalin arziki kaimi da kuma bayar da gudunmawa wajen karin samun lafiya da rashin zaman dar-dar da ma samu daidaito a duniyar baki daya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ana son a dinga yin allaurar riga-kafin maleriya

More News

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...

Hukumar NDLEA ta lalata sama da tan 300 na miyagun kwayoyi da aka kama a Legas da Ogun

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi nasarar lalata kilogiram 304,436 da lita 40,042 na haramtattun abubuwa da...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...