Gwamnatin jihar Zamfara ta fara biyan wasu ‘yan fansho da suka yi ritaya a jihar jimillar kuɗi naira biliyan 13.4.
Ku tuna cewa gwamnatin jihar ta kafa kwamiti don tantance bayanan ma’aikatan da suka yi ritaya don biyan basussukan da aka tara daga shekarar 2011 zuwa yau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Idris ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa wadanda suka yi ritaya suke ke bin bashin giratuti tun a shekarar 2011, daga karshe sun fara karbar kudadensu.
An fara biya tun ranar Alhamis.
“Gwamnatin jihar ta dauki wani muhimmin mataki na magance basussukan da ma’aikatan da suka yi ritaya suke bi, wanda ya hada da na mutuwa, gratuti na ritaya, da kuma na kwangila.”