Gwamnatin Uganda za ta haramta ‘cacar’ wasanni

Caca ta zama sana'a ga matasan kasar da yawa
Image caption

Gwamnatin kasar Uganda ta tabbatar da cewa ba za ta sake bai wa kamfanonin caca lasisi a fadin kasarta ba.

Wannan wani yunkuri ne da kasar ke yi domin hana caca a kasar kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito ministan tattalin arzikin kasar, David Bahati, yana cewa.

“Mun samu umurni ne daga shugaban kasa Yoweri Museveni da mu dakatar da cacar wasanni da kamfanonin caca.

Shugaban kasa ya bawa hukumar dake kula da su wannan umurni,” a cewar Mr Bahati.

Ministan ya bayyana cewa shugaban kasar ya bada wannan umurni ne sabado illar da caca ke haifarwa kanana yara a kasar.

Hakkin mallakar hoto
AFP
Image caption

Shugaban kasa Yoweri Museveni ne ya bada umurnin

Cacar wasannin kwallon kafa babbar sana’a ce a kasar kuma tana ci gaba da habbaka.

Matasa da yawa marassa aikin yi a kasar sun shiga harkar caca ne inda suke fatan gina rayuwarsu, kamar yadda BBC ta ruwaito a 2017.

“Daga yanzu, babu wani sabon kamfanin da za a yi wa rajista. Wadanda aka yi wa rajista ba za a sake ba su lasisi ba idan wa’adin sake lasisi yayi.”

Mr Bahati ya fada wa mutane a cikin cocin Rugarama dake garin Kabale.

Ya kuma bayyana cewa Fastocin coci dake adawa da cacar na iya yin murna a yanzu domin addu’arsu an karbe ta.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...