Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar hutun bikin samun ƴancin kai

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutun bikin tunawa da ranar da Najeriya ta samu ƴan cin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya..

Olabunmi Tunji-Ojo ministan harkokin cikin gida shi ya sanar da hotun a ranar Asabar a wata sanarwa da babbar sakatariyar dindin ta ma’aikatar, Magdalene  Ajani to ta fitar.

Ministan ya yabawa ƴan Najeriya dake da haƙuri da aiki tuƙuru inda ya ƙara da cewa sadaukarwa da suka nuna baza ta tafi haka kawai ba.

Ya kuma jaddada buƙatar ƴan Najeriya da suyi duba kan sadaukarwar da gwarazan da suka kafa ƙasar.

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa baza ayi bikin shagulgula sosai ba na tunawa da ranar saboda halin matsin rayuwa da al’umma suke fuskanta.

More News

Gwamnatin Enugu ta bayyana dalilin sanya haraji kan gawar mutane

Gwamnatin Jihar Enugu a ranar Lahadi tayi ƙarin haske kan matakin da ta ɗauka kan sanya haraji akan gawar mutane dake ajiye a ɗakin...

Ɗan tsohon gwamnan Kaduna Ahmad Makarfi ya rasu a hatsarin mota

Faisal Makarfi dan gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmad Muhammad Makarfi ya rasu. Faisal ya rasu a wani hatsarin mota da ya faru akan hanyar...

Ƴan sanda sun kama mutane 6 da ake zargi da kisan kai da fashi da makami a Gombe

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce a cikin mako guda  jami'an ta sun kama wasu mutane 6 da ake zargi da aikata fashi...

Ƴan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Gyaran Hali na Maiduguri

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce jami'an ta sun kama Kyari Kur ɗaya daga cikin ɗaurarrun da suka tsere daga gidan gyaran hali ...