Gwamnatin Najeriya za ta haramta kungiyar Shi’a ta IMN

Zakzaky
Image caption

Sheikh El-zakzaky ya ce ba zai fasa abin da yake yi ba

Gwamnatin Najeriya ta samu takardar hukuncin wata babbar kotu a Abuja da ke bayyana ayyukan kungiyar ‘yan Shi’a ta Islamic Movement In Nigeria da na ‘ta’addanci kuma haramtattu’.

Jaridar Punch Newspaper ce da ta ce ta samu damar ganin wannan takarda ce ta samu ganin wannan takardar inda ta ce ofishin ministan Shari’ar kasar ne ya nemi hukuncin a ranar Juma’a.

Takardar ta ce kotun da mai shari’a Nkeonye Maha ta jagoranci zamanta ta yanke cewa “Daga yanzu ba bu wani dalilin da zai sa a amince wa wasu mutane ko gungun mutane ba yin kira kansu da suna ‘yan Shi’a.”

Takardar ta kara da cewa kotun ta bayar da umarnin ne bayan da ta samu ‘takardar bukatar’ haramta kungiyar daga gwamnatin tarayya.

“Domin tabbatar da an haramata kungiyar, kotun ta umarci ministan Shari’a da ya bayyana hukuncin haramta kungiyar a kundin gwamnati da kuma manyan jaridun Najeriya guda biyu.” In ji takardar.

Ci gaba da zanga-zangar da ‘ya’yan kungiyar ke yi na neman a saki jagoransu da ke tsare a hannun gwamnati tun 2015, a Abuja da sauran sassan kasar na ci gaba da janyo asarar rayuka.

Ko a makon da ya gabata sai da ‘yan sanda suka ‘kashe’ ‘yan kungiyar 11 a Abuja a irin wannan zanga-zanga, inda su kuma ‘yan sanda suka yi zargin ‘yan kungiyar sun kashe babban jami’n ‘yan sanda.

Ana sa ran cewa fadar gwamnati ko kuma ma’aikatar Shari’a ce za ta sanar da wannan hukuncin na ‘haramta’ ayyukan kungiyar ta IMN.

Idan har ‘haramcin ya faru’, to IMN za ta zama kungiya ta biyu bayan IPOB da Shugaba Muhammadu Buhari ya haramta a mulkinsa.

A shekarar 2017 ne gwamnatin Buhari ya haramta ayyukan kungiyar masu fafutukar neman ballewar yankin kudu maso gabas na Najeriya daga kasar wato IPOB.

To sai dai kungiyar IMN na da hurumin daukaka kara kasancewar ba su da wakilici lokacin da aka fitar da wannan hukunci.

Sharhi, Usman Minjibir

Wannan takarda dai na zuwa ne a ranar da tsohon ministan Shari’ar kasar, Abubakar Malami ya bayyana gaban majalisar dokokin kasar domin a sake tantance a matsayin minista a gwamnatin Buhari.

An tambayi tsohon ministan na shari’a dalilin da ya sa ya ki amincewa a saki tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Sambo Dasuki da kuma jagoran ‘yan Shi’a a Najeriya Malam Ibrahim Zakzaky duk da kotu ta bayar da belinsu, sai ya ce hakkin ofishinsa ne ya kare hakkin ‘yan Najeriya ba na wani mutum daya ba.

Ya ce Kundin mulki na Najeriya sashi na 174, ya bayyana cewa hakkin ofishin ministan shari’a ne shi bada kariya da kuma shawara kan hakkin al’umma.

“Dole minista ya kula da hakkin ‘yan kasa ba hakkin mutum daya tilo ba,” in ji shi.

Ana dai zargin gwamnatin Najeriya da kin mutunta hukuncin wasu kotuna da suka bayar da belin Sambo Dasuki da kuma Malam Zakzaky.

Amma Malami ya ce idan mutum daya ko biyo ko uku suka yi kokarin tayar da hankalin ‘yan kasa wajibi ne a yi maganinsu ta hanyar daukar mataki na shari’a.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Har wa yau, ita wannan takarda da jaridar Punch Newspaper ce da ta ce ta samu damar ganin wannan takarda ta buga na zuwa ne kwana uku kafin sake bayyanar shugaban kungiyar ta IMN, Sheikh Ibrahim Elzakzaky a kotu da ke zama a jihar Kaduna.

El-zakzaky da mai dakinsa dai na neman samun beli domin fita kasar waje neman lafiya kasancewar suna cikin ‘matsanancin’ hali na rashin lafiya.

Kotun dai ce ta dage sauraren bukatar neman belin a zamanta na ranar 18 ga watan Yuli har zuwa 29 ga watan na Yuli.

Tana iya yiwuwa gwamnati ta nemi a ‘haramta’ kungiyar ne domin yin amfani da hakan a gaban kotu.

Watakila kuma an samu hukuncin ‘haramta’ ayyukan kungiyar domin yin kandagarki na abin da zai je ya zo a ranar Litinin din, ranar da ake sa ran kotun ta Kaduna za ta yanke wannan hukunci.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...