Gwamnatin Buhari Da Ta Abacha Duk Abu Daya Ne, Inji Obasanjo

Cif Olusegun Obasanjo, a jawabinsa da ya yi daga dakin karatunsa a garin Otta na Jihar Ogun, ya yi ikirarin cewa shugaba Buhari ya yaudari ‘yan Najeriya da aka zabe shi a karo na farko, don haka ba daidai ba ne ‘yan Najeriya su sake ba da irin wannan dama.

A cikin wasika da ya rubuta ya kafa hujja da bayanan sakataren tsohuwar jam’iyyar shugaba Buhari, wato CPC Injiniya Buba Galadima ya ce Buharin ba ya daukar shawara.

Muryar Amurka ta tuntubi Buba Galadima don jin martanin sa kan wannan batun, inda ya tabbatar da cewa hakan gaskiya ne.

Kazalika Obasanjo ya yi magana kan zargin hukumar zabe ba ta da niyyar yin zaben adalci ko kuma shugaba Buhari na son dawowa mulki ko ta halin kaka.

A bayaninsa kan batun, Buba Galadima ya yi a matsayin sa na kakakin kamfen na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ya ce rashin sanya hannu kan dokar zabe da neman gurfanar da bababn alkali Walter Onnoghen gaban kotu shaidu ne na rashin adalcin.

Yanzu dai ya rage kasa da wata daya a gudanar da babban zaben a ranar 16 ga watan gobe.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...