Gwamna Inuwa ya kaddamar da rabon takin zamani mai sauƙin farashi

Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya kaddamar da fara sayarwa tare da raba takin zamani.

Da yake magana a ranar Litinin a wurin kaddamarwar a karamar hukumar Akko, Yahaya ya sanar da ragin kaso 25 kan yadda ake sayar da takin a kasuwa.

Ya ce ragin yasa farashin takin ya koma 19000 daga 26000 kuma an yi shi ne domin rage wa manoman nauyi.

“Gwamnati ta sayo motoci 160 kimanin metric tan 5000 kan kuɗi naira biliyan biyu da miliyan ɗari takwas da talatin da bakwai da dubu ɗari biyar (N2,837,500,000.00) ƙarin motoci 35 kan yawan wanda aka saya bara, ” ya ce .

Gwamnan ya tabbatarwa da monoman cewa an tanadi matakai da za su tabbatar takin ya isa ga manoma.

More from this stream

Recomended