Connect with us

Hausa

Gobara ta kama Ofishin INEC a Filato

Hukumar Zabe

Hakkin mallakar hoto
INEC

Image caption

An kona daya daga cikin ofishin hukumar zabe a Najeriya kwanaki shida kacal kafin gudanar da babban zabe a kasar.

Gobarar dai ta faru ne a ofishin hukumar a jihar Filato dake arewacin kasar inda muhimman kayayyakin zabe kamar akwatuna da takardun jefa kuri’a suka kone.

Mai magana da yawun hukumar ya bayyana kona ofishin a matsayin mayar da hannun agogo baya a bangaren shirye-shiryen zabe.

A wata sanarwa da hukumar zaben ta fitar ta bayyana cewa wannan ne karo na biyu da aka samu konewar ofishinta a cikin wannan watan, inda tayi kira ga jami’an tsaro a kasar da su kara matse kaimi wajen ba ofisoshinsu tsaro.

Ana sa ran dai za a gudanar da babban zabe a kasar a ranar Asabar.

A ranar lahadi ne dai shugaban kasar Muhammadu Buhari yayi gargadi a kan magudin zabe.

A wani bangaren kuma, shugaban ya koka a kan zargin da hukmar EFCC a kasar tayi na makudan kudaden da ake fitarwa ba bisa ka’ida ba domin siyan kuri’a.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Ban ce Buhari ya sauka daga kujerar mulkinsa ba – IBB

Janar Ibrahim Badamasi Babangida, tsohon shugaban mulkin soja, ya yi watsi da labaran da ake yadawa ta kafar Intanet dake cewa ya shawarci shugaban kasa Muhammad Buhari ya sauka daga kan mulki.

Babangida a wata sanarwa da ofishinsa na yada labarai ya fitar ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar bai mallaki wani shafi ba na kafafen sadarwar zamani ballantana ya yi amfani da kafar wajen bayyana ra’ayinsa kan abinda ke faruwa a ƙasarnan.

Sanarwar ta ce an jawo hankalin tsohon shugaban kasar kan wani shafi na kafar sadarwar Twitter da kuma sauran kafafen sadarwar zamani mai dauke da suna tsohon shugaban kasar.

Ta kuma shawarci jama’a musamman masu amfani da kafar sadarwar zamani ta Twitter cewa tsohon shugaban bashi da shafi a kafar ko kuma kowace kafar sadarwar zamani.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

INEC ta amince jam’iyu su cigaba da yakin neman zabe

Hukumar Zabe ta kasa INEC, ta ce a yanzu jam’iyun siyasa za su iya cigaba da yakin neman zabe gabanin sabuwar ranar da aka saka ta zaben shugaban kasa.

Hukumar ta bayar da wannan umarnin ne bayan wani taro da tayi ranar Litinin a Abuja.

Tun da farko shugaban hukumar, Mahmoud Yakubu ya ce ba za a cigaba da yakin neman zabe ba duk da dage ranar zaben shugaban kasa da na yan majalisun tarayya da aka yi.

Amma kuma bayan zaman ganawar da shugabannin hukumar suka yi hukumar ta ce yan takarar shugaban kasa da kuma jam’iyun siyasa za su cigaba da yakin neman zabe har ya zuwa daren ranar Alhamis.

Ko da a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC da ta gudanar a yau jam’iyar taci alwashin cigaba da yakin neman zabe duk da cewa hakan yaci karo da umarnin INEC.

Dokar zabe ta bayyana za a dakatar da yakin neman zabe ne sa’o’i 24 gabanin a fara kada kuri’a.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Sheikh Giro ya nemi afuwar ‘yan Najeriya game da tsine wa “makiyan” Buhari

Malamin Izala a Najeriya, Shiek Abubakar Giro Argungu, ya nemi afuwar ‘yan Najeriya a kan wani bidiyo da yake nuna malamin yana kakkausan kalamai a kan “makiya” Shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Malamin ya bayyana cewa bidiyon an nade shi ne tun a 2015 kuma ya yi kalaman ne sakamakon wata matsala da ta faru a siyasar wancan lokaci.

Bidiyon dai ya nuna Malamin yana kwashewa marasa goyon bayan Buhari albarka sa’annan ya yi wa marasa ci gaban Najeriya fatan hatsarin mota.

Sheik Abubakar ya ce ya yi nadamar yin wadannan kalamai kuma ya amince da kuskurensa.

Malamin ya ce a wancan lokaci ya yi raddi ne ga wata kabila mai suna ‘yan tatsine.

Tun bayan da guguwar siyasar 2019 ta fara kadawa a Najeriyar aka samu rarrabuwar kai na malamai musamman na Izala a kasar.

A kwanakin baya an samu sabanin ra’ayi da Sheik Ahmed Gumi wanda daya daga cikin Malaman Izala ne a kasar.

Haka a wani bangaren an samu sabanin ra’ayi da Shiek Yusuf Sambo Rigachikun bayan ya bayyana ra’ayinsa na goyon bayan dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: