Gobara ta ƙone kayayyaki na miliyoyin naira a Lagos

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas LASEMA ta ce kayayyaki na miliyoyin Naira ne suka ƙone a wata gobara da ta kama shagon sayan da kayan lantarki na LG.

Olufemi Oke-Osanyintolu darakta janar na hukumar ta LASEMA ya ce lamarin  ya faru ne a kasuwar Trade Fair a unguwar Abule Osun dake birnin.

Ya ce hukumar ta samu kiran kai ɗaukin gaggawa da misalin ƙarfe 12:15 na dare.

Jami’an hukumar sun samu nasarar isa wurin da lamarin ya faru da karfe 12:40 inda suka samu wutar tana ci ganga-ganga.

Gobarar ta samu nasarar bazuwa zuwa cikin ginin baki ɗaya.

Oke-Osanyintolu ya ce hukumar tare da jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Lagos sun samu nasarar shawo kan gobarar.

More from this stream

Recomended