Ganduje ya bai wa ‘yan bautar kasar da aka yi wa fashi naira dubu dari-dari

Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Kano, ya raba wa ‘yan bautar kasa guda 6 da ‘yan fashi su ka kaiwa hari, N600,000.

Gwamnan wanda ya bada kyautar a ranar juma’a 29 ga watan Maris, ya ce ya ba da kudin ne saboda ya kwantarwa da wadanda abin ya shafa hankali. Sannan Gandujen ya roki ‘yan bautar kasar da su zamanto mutane na gari, wadanda al’ummar baya da kasa zata yi alfahari da su.
Ganduje ya rabawa ‘yan bautar kasa dubu dari – dari

Sannan ya yiwa ‘yan bautar kasar alkawarin ba su tsaro yadda ya kamata a fadin jihar Kano, sannan ya yi musu alkawarin zai cigaba da basu alawus na N5,000 da ya saba basu duk karshen wata.

Sannan ya kara da cewa, ma’aikatan fannin lafiya, za a ba su alawus fiye da na kowa.

Ba dadewa, mu ka samu rahoton cewa ‘yan fashi sun kaiwa wasu masu bautar kasa su 6 hari, akan hanyar Gwarzo zuwa Karaye.

More News

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

Ɗan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...

Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu'a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da 'yan Najeriya ke ciki...