Fashewar Wasu Abubuwa Ta Jawo Mummunar Ɓarna A Birnin Ibadan

Fashewar wasu abubuwa ta janyo mummunan ɓarna a wasu unguwanni dake birnin Ibadan.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:45 na ranar Talata a yankin Bodija dake birnin kamar yadda gwamnan jihar Seyi Makinde ya bayyana.

Da yake magana da ƴan jaridu, Seyi Makinde ya ce akalla mutane 77 ne suka jikkata a fashewar abubuwan da ya alaƙanta da masu haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Mutane biyu aka tabbatar da mutuwar su kawo yanzu.

More from this stream

Recomended