
Farashin ɗanyen man fetur ya karu sosai a ranar Alhamis inda aka rika sayar da kowacce ganga kan dalar Amurka $97.
Farashin man nau’in Brent ya yi sama da kaso 3.6 cikin ɗari $97 kowacce ganga daga dala $94.30 a yadda aka rika sayar da shi a ranar Litinin.
Farashin da ake sayar da shi a yanzu shi ne mafi tsada tun watan Nuwamba na shekarar 2022.
An samu karin farashin ne sakamakon raguwar yawan ɗanyen man da kasar Amurka ke tarawa a rumbunta na musamman da kuma fargabar rage yawan man da kasashen kungiyar OPEC ke samarwa a kasuwar duniya.
Yawan man da Amurka take da shi da shi a ajiye ganga miliyan 416.3 ya ragu da ganga miliyan 2.2 kamar yadda alkaluman kididdigar da gwamnatin ƙasar ta fitar suka nuna.