Everton ta lallasa Man United

Premier

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Manchester United ta debi kashinta a hannu bayan Everton lallasa ta 4-0 a wasan mako na 35 a Premier da suka fafata ranar Lahadi a Goodison Park.

Everton ta ci kwallo biyu tun kan aje hutun rabin lokaci ta hannun Richarlison de Andrade da kuma Idrissa Gueye.

Bayan da suka koma zagaye na biyu aka kara zura kwallo biyu a ragar United ta hannun Lucas Digne da kuma Theo Walcott.

United, wadda ta buga karawar kamar ‘yan wasanta ba su da lafiya ta samu dama daya kacal da ta buga kwallo ta nufi raga saura minti hutu a tashi daga fafatawar.

Marcus Rashford ne ya samu damar a cikin masu tsaron bayan Evrton, ya kuma buga kwallo ta wuce saman kan mai tsaron raga Jordan Pickford.

Wannan nasarar ta kai Everton zuwa mataki na bakwai a teburin Premier, hakan zai iya kai ta gasar Europa a badi, ita kuwa United ta ci gaba da zama a matakinta na shida.

Sauran maki biyu ne tsakanin United da Arsenal ta biyar a teburi, wadda za ta fafata da Crystal Palace ranar Lahadi.

A ranar Talata ne Barcelona ta fitar da Manchester United daga gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana, kuma ba ta kai bantenta a FA Cup ba, kuma Manchester City ce ta lashe Caraboa Cup na shekarar nan.

Everton ta taba cin United 3-0 a gasar Premier ranar Lahadi 26 ga watan Afirilun 2015 a Goodison Park.

Yadda kungiyoyin suka murza-leda.

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...