EFCC Za Ta Daukaka Ƙara Kan Hukuncin Kotun Da Ya ce Ta Biya Emefiele Miliyan 100

Hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta yi watsi da hukuncin tarar naira miliyan 100 da kotun babban birnin tarayya Abuja ta yiwa hukumar kan yadda aka keta yancin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele.

Emefiele ya shigar da karar gwamnatin tarayya, antoni janar da kuma hukumar EFCC domin tabbatar da yancinsa a matsayinsa dan dam.

Ya ce duk da umarnin da kotu ya bayar da a sake shi an cigaba da tsare shi.

A ranar Litinin ne babbar kotun ta bayar da umarnin gwamnatin tarayya da kuma hukumar EFCC su biya Emefiele naira miliyan 100 kan yadda aka keta yancinsa na dan adam.

Da yake mayar da martani cikin wata sanarwa, Dele Oyewale mai magana da yawun EFCC ya ce kotun ta gaza lura da cewa kotu ce ta bayar da umarnin a tsare Emefiele.

Inda ya ce tabbas za su tunkari kotun daukaka kara domin ta jingine hukuncin.

More from this stream

Recomended