Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kama shugaban Faith On The Rock Ministry International, Theophilus Ebonyi, bisa zargin damfarar ’yan cocinsa da wasu ‘yan Najeriya.
Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja, ya ce an kama faston ne da laifin yin amfani da tallafin jabu daga gidauniyar Ford wanda ya kai N1,319,040,274.31.
Sanarwar ta kara da cewa, “An kama Ebonyi ne da laifin damfarar wadanda abin ya shafa, da suka hada da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma daidaikun jama’a ta hanyar tallata wani shirin tallafi ta wata kungiyarsa mai zaman kanta, Theobarth Global Foundation, yana mai ikirarin cewa gidauniyar Ford tana bayar da tallafin dala biliyan 20 don taimaka wa masu karamin karfi.
“An yi zargin cewa ya yaudare su don su yi rajista a matsayin wadanda suka ci gajiyar tallafin ta hanyar neman su biya kudin fom din rajista.
“Kowanensu an sanya shi ya biya N1,800,000
“Ta wannan tsari, an yi zargin Ebonyi ya ci N1,391,040, 274.31.”