Duniya ta fara shaida illar harin da aka kai wa Saudiyya | BBC Hausa

An ga hayaki ya turnuke bayan harin da aka kai kan wurin hakar mai na Armco da ke garin Abqaiq
Hakkin mallakar hoto
Reuters

Farashin mai ya yi tashin da bai taba yin irin sa ba cikin wata 4, bayan wasu hare-hare 2 da aka kai wa wurin hakar man kasar Saudiyya, wanda hakan ya sa aka samu nakasu na kashi 5 cikin dari na albarkatun mai da ake samarwa a duniya.

Gangar danyen mai ta Brent ta tashi da kashi 19 cikin 100 inda ta kai Dala 71.95 kan kowace ganga.

Duk da dai an samu sauki kadan bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umurnin fito da mai daga rumbunan kasar ta Amurka.

Zai dai iya daukan wasu makonni masu zuwa kafin matatar man ta Saudiyya da abin ya shafa ta dawo aiki yadda ta saba.

Kamfanin tace mai na kasar Saudi Aramco ya ce harin ya sanya man da kasar ke samarwa ya yi kasa da ganga miliyan 5.7 a kowace rana.

Harin wanda aka kai da jirgi maras matuki ya hada har da wanda ya fada kan matatar mai mafi girma a duniya da ke kasar ta Saudiyya.

Amurka dai ta zargi Iran da hannu a harin.

Saudiyya dai ta ce tana kokarin kashe wutar, to amma da alama kokarin nata bai isa ba – Inji Abishek Kumar, wani jami’i a Interfax Energy.

Ya kara da cewa da alama barnar da aka yi wa cibiyoyin sarrafa man fetur din na Abqaiq da Khurais na da muni.

Iran ta zargi Amurka da kokarin yaudara, bayan da sakataren wan=jen Amurka din Mike Pompeo ya ce Iran ce ke da alhakin kai harin.

Mr Pompeo dai ya yi watsi da ikirarin da ‘yan tawayen Houthi na Yemen suka yi cewa su ne ke da alhakin kai harin.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...