Dokar wa’azi a ta janyo takaddama a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufa'i

Hakkin mallakar hoto
www.independent.ng

A jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya wata doka da majalisar dokokin jihar ta amince da ita wadda za ta kayyade yadda malaman addini ke gudanar da wa’azi ta fara janyo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen jihar.

Yanzu haka dai tuni wasu malamai da kuma kungiyoyi suka fara sukar lamirin yin garambawul ga dokar.

Dokar wadda majalisar dokokin jihar ta Kaduna ta amince da ita, an kirkireta ne tun a shekarar 1984, inda ta kafa wasu ka’idoji kan yadda masu wa’azi za su rinka yin wa’azi.

Tun a lokacin da gwamnatin jihar ta fara ikirarin farfado da wannan doka, wasu bangarori sun rinka yin alawadai da ita.

Sheikh Dahiru Maraya, malamin adiinin musulunci ne a Kaduna, ya kuma shaida wa BBC cewa, ta bangaren batun samun lasisi kafin mutum ya fara wa’azi ma kadai, dokar ta sabawa tsarin mulkin Najeriya.

Ya ce baya ga wannan dalili, dokar kanta ta sabawa addinin musulunci saboda Manzon Allah (SAW) ya ce, ‘ Ku isar da sako daga gareni ko da daya ne’.

Sheikh Dahiru Maraya, ya ce to tun da har Annabin Allah ya bayar da umarni, a matsayin mutum musulmi ba bu abinda yakamata ya yi illa ya bi umarnin ba ai wani ya baka lasisi ba.

Ya ce to saboda wadannan dalilai ne, ba su yarda da wannan bangare na wannan doka da majalisar jihar ta Kaduna ta amince da ita.

Ita ma kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kaduna wato CAN , ta ce wannan doka ba bu wani alfanu da za ta kawowa al’ummar jihar.

Rabaran Dr Sunday Ibrahim, shi ne sakataren kungiyar ta CAN, a jihar, ya shaida wa BBC cewa, su tuni sun shaida wa gwamnatin jihar cewa kowacce majami’a na da nata tsarin domin mutum ba ya fara wa’azi har sai ya bi ko cik wasu matakai.

Don haka batun ace har sai an ba wa mutum lasisi zai fara wa’azi, gaskiya ba su amince da shi ba, don haka sam ba sa goyon bayan wannan doka.

Ita dai gwamnatin ta jihar Kaduna wadda ta bullo da wannan doka, ta ce wadanda suke sukar wannan doka, sun yi mata gurguwar fahimta ce.

Gwamnatin ta ce, ba a bullo da wannan doka don a raba kawuna ko kuma kawo matsaloli a cikin al’umma ba.

Don ba bu wani dalili da za a ce ya janyo ce-ce-ku-ce a kan dokar ba.

Gwamnatin jihar ta ce ta yi hakan ne domin inganta zaman lafiya a jihar.

Kaduna dai na daga cikin jihohin Najeriya da suka sha fama da rigingimu na addini da kabilanci, abinda ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi masu dinbin yawa.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...