Dino Melaye ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutane

[ad_1]








Sanata Dino Melaye, dan majalisar dattawa dake wakiltar mazabar yammacin Kogi ya sanar da tserewarsa daga hannun masu garkuwa da mutane.

A jiya ne aka rawaito cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da shi akan hanyar Abuja zuwa Lokoja da safiyar ranar Alhamis.

Melaye na kan hanyarsa ta zuwa Kogi domin halartar zaman wata kotun majistire dake Lokoja.

Ana dai tuhumar Melaye da laifin safarar bindigogi.

Da yake bayyana abin da ya faru dan majalisar ya fadi cewa ya shafe sa’o’i 11 cikin fargaba da kaduwa lokacin da yake hannun masu garkuwa da mutane.

Sai dai rundunar Æ´ansandan Najeriya ta ce bata samu rahoto ba game da sace dan majalisar inda ta nemi duk wanda yake wurin lokacin da abin yafaru da ya kai kansa ga yansanda domin ya taimaka ga bayanan da za su taimaka a ceto dan majalisar.

Yan Najeriya da dama dai na ganin dan majalisar shine ya shirya yin garkuwa da kansa inda suke ganin garkuwar tamkar wani wasan kwaikwayo ne da ya shirya.




[ad_2]

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...