Darajar naira tayi ƙasa a kasuwar musayar kuɗaɗe

Darajar takardar kudin Naira tayi ƙasa a ranar Litinin inda aka riƙa canza dalar Amurka ɗaya kan ₦1612 a kasuwar musayar kuɗaɗe ta gwamnati.

Wannan farashin shi ne mafi karanci tun daga na ranar 04 ga watan Disambar 2024 inda aka sayar da dalar Amurka akan ₦1613.69.

A kasuwar musayar kuɗaɗe ta gwamnati NFEM darajar naira tayi ƙasa da kaso 2.89 cikin ɗari wato ya zuwa ₦1612.23 idan aka kwatanta da ₦1567.02 da aka riƙa sayar da ita a ranar 04 ga watan Afrilu .

A kasuwar musayar kuɗaɗen ƙasar waje ta bayan fage takardar kuɗin ta naira tayi ƙasa da kaso 3.51 a cikin dari ya zuwa ₦1620 kan kowace dala a ranar 08 ga watan Afrilu idan aka kwatanta da ₦1565 da aka rika sayarwa a ranar 07 ga wata.

More from this stream

Recomended