Dan bindiga ya bude wuta a jirgin kasa

Shooting in Utrecht 18 March 2019

‘Yan sanda masu yaki da ta’addanci a wurin da aka kai harin

Wani dan bindiga ya bude wuta a cikin wani jirgin kasa a birnin Utretch da ke kasar Netherlands

Mutane da yawa sun samu raunuka kuma ana tunanin daya ya mutu a harbin da aka yi da misalin karfe goma da minti arba’in da biyar agogon kasar wato karfe tara da minti arba’in da biyar kenan agogon a kusa da titin Oktoberplein.

‘Yan sanda sun ce dan bindigar ya tsere. An dakatar da ayyukan jiragen kasa kuma an umarci makarantu da su rufe kofofinsu.

‘Yan Sandan da ke yaki da ta’addanci sun bayyana cewa “harin ta’addanci ne”.

Firayim ministan kasar Mark Rutte ya ce ya shiga matsananciyar damuwa kuma ya soke zaman tattaunawarsa da sauran jami’an gwamnati na mako-mako.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun umarci babban asibitin koyarwa na Utrecht da ya bude dukkan dakunan bayar da taimakon gaggawa don kula da wadanda suka samu raunuka.

Wani ganau ya bayyana wa manema labarai cewa “wani mutum ne ya fara harbi ta ko’ina”.

Wani kuma ya bayyana cewa ya ga wata mace da jini a hannuwanta da kayanta.

“Na sanya ta a cikin motata na taimake ta,” ya ce. “Lokacin da ‘yan sanda suka iso wurin, ba ta cikin hayyacinta.”

Babu tabbas kan yawan mutanen da suka yi rauni ko kuma girman raunukan da suka samu.

[ad_2]

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...